Da dumi-dumi: Kabiru Gaya ya jagoranci sayawa Osinbajo Fom din takara N100m

Da dumi-dumi: Kabiru Gaya ya jagoranci sayawa Osinbajo Fom din takara N100m

Abuja - An sayawa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Fom din takara kujeran shugaban kasa ranar Alhamis, 5 ga Mayu, 2022 a birnin tarayya Abuja.

Fom din, wanda aka saya N100m zai baiwa mataimakin shugaban kasan daman takarar zaben tsayar da gwani karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu, Kabiru Gaya, ne ya jagoranci saya Fom, rahoton ChannelsTV.

Kabiru Gaya ne shugaban kungiyoyin magoya bayan Yemi Osinbajo.

Kabiru Gaya da Fom din takara N100m
Da dumi-dumi: Kabiru Gaya ya jagoranci sayawa Osinbajo Fom din takara N100m Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel