'Yan Hayar Gidana Su Na Yunƙurin Ganin Baya Na, Mai Gidan Haya Ya Fada Wa Kotu

'Yan Hayar Gidana Su Na Yunƙurin Ganin Baya Na, Mai Gidan Haya Ya Fada Wa Kotu

  • Abdulwaheed Akani, wani mazaunin Ibadan wanda ya ke da gidan haya, ya bayyana a kotu ranar Juma’a a inda ya kai karar ‘yan hayar gidansa
  • A cewar Akani, Oluwatosin Ogunbadejo da Blessing Olapade su na yunkurin kai shi kabari kafin lokacinsa ta hanyar kin bin dokokin tsaro
  • Akani ya bayyana yadda Ogunbadejo ya taba shiga har dakinsa ya buga masa wani abu a kansa har sai da wani makwabcinsu ya cece shi saboda rashin jituwa

Ibadan - Wani mai gidan haya, Abdulwaheed Akani, a ranar Juma’a ya bayyana gaban wata kotu a Ibadan inda ya kai karar ‘yan hayar gidansa, Oluwatosin Ogunbadejo da Blessing Olapade, inda ya ce su na yunkurin ganin bayansa, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

Yayin kai korafin ga kotu, Akani ya zargi Ogunbadejo (namiji) da Olapade (mace) da cutar da shi ta hanyar kin bin dokokin tsaron da aka shimfida a yankinsu.

'Yan Hayar Gidana Su Na Yunƙurin Ganin Baya Na, Mai Gidan Haya Ya Fada Wa Kotu
'Yan Hayar Gidana Su Na Kokarin Ganin Baya Na, Mai Gidan Haya Ya Fada Wa Kotu. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

Mai karar, wanda lauyansa, A.B. Bello ya jagorance shi gaban kotun ya ce a ranar 1 ga watan Oktoban 2021 ‘yan hayar guda biyu su ka amince da kasancewa masu bin doka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce har farmaki su na kai masa

A cewarsa kamar yadda Premium Times ta nuna:

“Saboda matsalar tsaro musamman ta batun ‘yan fashi da makami da kuma kungiyar asiri, an yi yarjejeniya da DPO din ofishin ‘yan sanda na Sango cewa ko wanne mazaunin yankin zai dinga rufe kofarsa daidai karfe 10 na dare.
“Sai dai wadanda ake karar sun ki bin dokar. Ogunbadejo ya zarge ni da barin kofar baya a bude wacce ta ke kusa da dakinsa.

Kara karanta wannan

An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

“Daga nan ne ya shigo har dakina inda ya buga min wani abu a kaina. Sai da wata makwabciyarmu ta zo don ceto na yayin da ta dinga rokon shi ya bar ni haka.”

Mutumin ya kara da shaida yadda Olapade, dayar wacce ya ke kara, matar dan sanda ce, wanda hakan ya sa ta ke rashin mutunci yadda ta ga dama.

Duk ba su bayyaa gaban kotun ba

Ya bayyana yadda ta kai masa farmaki har sau biyu, hakan ya sa ya kai kararta ofishin ‘yan sanda na Sango amma ba a yi mata komai ba.

Ya bukaci kotu ta tilasta wadanda ya ke kara da su biya kudin magungunan shi inda ya gabatar wa kotun da bidiyo da sautin murya na irin cutar da shi da suka yi.

Sai dai duk wadanda ya ke karar ba su bayyana gaban kotu ba hakan ya sa Alkalin kotun, S.M. Akintayo ya bukaci duk a gabatar da su da shaidu gaban kotu.

Kara karanta wannan

Babbar matsala ta Buhari 1 ne, kuma babu abin da ya tabuka a cikin shekaru 7 inji Yakasai

Alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Yuni don ci gaba da sauraron karar.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164