Ramadaniyyat 1443: Dogaro Ga Allah, Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo

Ramadaniyyat 1443: Dogaro Ga Allah, Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

A cikin jeringiyar janyo hankali na watar Ramadana da Malam ya yiwa lakabi da Ramadaniyyat, ya yi tsokaci kan dogaro ga Allah.

Dogaro Ga Allah (SWT)

1. Umarni da dogaro ga Allah da yabon masu dogaro ya maimatu a cikin Alƙur'ani a wurare da yawa, kimanin wuri (70). Wannan yana nuna mana girman mahimmancin wannan ibada ta dogaro ga Allah (SWT).

2. Allah (SWT) ya cancanci a dogara gare shi, saboda siffantuwarsa da duk siffofi na kamala, kamar cikar iliminsa da yalwar rahamarsa da cikar ƙudurarsa da buwayar mulkinsa, da kyakkyawar hikimarsa da sauransu.

3. Babu wanda ya kai annabawan Allah dogaro ga Mahaliccinsu cikin dukkan al'amuran rayuwarsu, wannan ya sa nasarar Allah ta zamo tare da su a koyaushe. Suka zamo abin koyi ga 'yan baya, ababen alfahari ga mutanen kiriki.

Kara karanta wannan

Sallah: Tinubu ya gwangwaje Musulmai da buhunan shinkafa 3,000 a Nasarawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

4. Bawa yakan dogara da Mahaliccinsa saboda ya yi imani da shi, ya kuma yi imani da ƙadarrarsa, tare kyautata zato a gare shi koyaushe.

5. Dogarar bawa ga Allah (SWT) ba za ta cika ba, sai tare da cikakken kyautata zato ga Allah (SWT). Bawa ya yi imani cewa, Allah (SWT) mai taimakonsa ne matuƙar ya kasance mai gaskiya wajen tsayuwa da umarninsa da kiyaye dokokinsa da yarda da kyakkyawan zaɓinsa. Idan zaton bawa ga Ubangijinsa ya munana, to a kan rasa dogaro da Allah a tare da shi.

6. Duk mai dogaro ga Allah (SWT) zai cimma manyan nasarori a ruyarsa kamar haka:

• Samun soyayyar Allah a gare shi.

• Dacewa da kulawar Ubangijinsa a gare shi.

• Kuɓuta daga wulaƙanta ta tozarta a duniya da lahira.

• Kuɓuta daga makircin Shaiɗan da sharrinsa.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Sanatan APC Okorocha ya karbi fom din takarar shugaban kasa a zaben 2023

• Kuɓuta daga damuwa da ɓacin rai.

• Kuɓuta daga azabar Allah da kamunsa mai tsanani.

• Samun shiga gidan Aljanna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng