Bakano ya rasa ransa bayan ya shiga masai tsamo wayarsa da ta fada

Bakano ya rasa ransa bayan ya shiga masai tsamo wayarsa da ta fada

  • Wani mutumi mai shekaru 40 ya rasa ransa bayan ya yi yunkurin ciro wayarsa da ta fada masai a Jirgiya a karamar hukumar Nassarawa dake Kano
  • An gano yadda Mu'azu Garba, dan asalin jihar Katsina ya shiga ramin masai don ciro wayarsa, amma ya kasa fitowa, daga bisani aka ceto shi ranga-ranga, sannan rai ya yi halinsa
  • Ko lokacin da 'yan kwana-kwana suka isa wurin sun tarar da gawar mutumin daga baya suka mika gawarsa ga shugaban gundumar Jigirya

Kano - A ranar Alhamis wani mutum 'dan shekara 40 mai suna Muazu Garba, ya rasa rayuwarsa yayin da ya yi kokarin ciro wayarsa, wacce ta fada masai a Jirgiya Quarters a karamar hukumar Nassarawa dake jihar Kano, rahoton Within Nigeria ya bayyana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Za Ta Siyo Jiragen Sama Don Yaƙi Da Wutar Daji, Ministan Harkokin Gida, Aregbesola

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga The Punch, ya ce:

Bakano ya rasa ransa bayan ya shiga masai tsamo wayarsa da ta fada
Bakano ya rasa ransa bayan ya shiga masai tsamo wayarsa da ta fada. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

"A ranar Alhamis, 28 ga watan Afirilu, hukumarmu ta samu kiran gaggawa daga wani Abbas Abubakar, wanda ya shaida mana aukuwar lamarin a Jirgiya ta karamar hukumar Nassarawa.
"Jami'anmu sun isa wurin, inda suka gano wani mutum shekaru 40, Mu'azu Garba, dan asalin jihar Katsina, ya shiga cikin ramin masai da niyyar ciro wayarsa da ta fada. Sanadin haka ne, wanda lamarin ya auku da shi ya fada, aka cetoshi ranga-ranga, daga bisani rai ya yi halinsa.
"Mun riga mun mika gawarsa ga shugaban gundumar Jigirya, Nuhu Adamu, sai dai an gano musabbabin mutawar na da alaka da kokarin ciro wayar da ya yi a ramin masan."

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Kanam: Yadda gwamna Lalong ya yi watsi da gargadin da nayi masa – Shugaban karamar hukuma

Bidiyon yadda fasinja ta yanke jiki ta fadi, tace ga garinku a filin jirgin sama dake Abuja

A wani labari na daban, wata fasinjar jirgin sama, wacce aka fi sa ni da Mama Tobi ta yanke jiki ta fadi inda ta mutu a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, wani lauya mai suna Che Oyinatumba ne ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ganau din ya wallafa bidiyoyin a shafinsa na Facebook, inda ya nuna yadda lamarin ya auku. Kamar yadda bidiyon ke nunawa, an ga wasu fasinjoji na yi wa matar da ba a san ko wacece ba addu'o'i bayan ta yanke jiki ta fadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: