Fusatattun Matasa sun fitittiki Sanata a mazabarta a Jos, sun kona motar yan jarida

Fusatattun Matasa sun fitittiki Sanata a mazabarta a Jos, sun kona motar yan jarida

  • Kuma dai, wasu matasa sun fitittiki wata yar majalisa bisa rashin wakilcin kwarai tsawon shekaru 3
  • Yar majalisar ta ziyarci yankin kaddamar da wasu ayyuka da suka yi amma matasan basu gamsu ba
  • Fusatattun matasan sun kona motar yar majalisar tare da motar yan jaridan da suka raka ta daukan rahoto

Plateau - Sanata mai wakiltar mazabar Plateau South, Nora Ladi Dadu'ut, tare da hadimanta da wasu yan jarida sun tsallake rijiya da baya yayinda fusatattun matasa suka kai mata hari.

Wannan hari ya auku ne ranar Alhamis a unguwar Namu, karamar hukumar Quaan Pan ta jihar, rahoton TVCNews.

Harin ya auku ne jim kadan bayan Sanatar ta kaddamar dakin karatun yanar gizo a unguwar.

Matasan sun bankawa motar Sanatar da motar kungiyar yan jaridar jihar NUJ wuta kurmus.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruwan sama, ana tantance Atiku, Saraki da sauran yan takara a PDP

TVC ta tattaro cewa jami'an tsaro sun dira unguwar kuma sun kama matasa hudu.

Sakamakon haka sauran matasan sun tare hanya suka ce Sanatar ba zata wuce ba sai an sako matasan da aka kama.

Daga karshe jami'an Sojojin Operation Safe Haven suka kwaceta da kyar daga hannunsu.

Kawo yanzu an kafa dokar hana fita a unguwar.

Fusatattun Matasa sun fitittiki Sanata a mazabarta a Jos, sun kona motar yan jarida
Fusatattun Matasa sun fitittiki Sanata a mazabarta a Jos, sun kona motar yan jarida Hoto: Tvcnewsng
Asali: Facebook

Bidiyon yadda matasa suka fattataki wani dan majalisar jiha tare da yi masa ihu a mazabarsa

A wani labarin kuwa, wani dan majalisar dokokin jihar Ondo, Mista Oluwole Ogunmolasuyi, ya gamu da fushin al’ummar mazabarsa inda suka kai masa farmaki kan zargin rashin yi masu aiki.

Ogunmolasuyi ya kasance dan majalisa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai wakiltan mazabar Owo 1 kuma shine shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin na jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

Wani mai amfani da shafin Facebook, Tosin Fapohunda II, ne ya wallafa bidiyo wanda a ciki ne aka farmaki dan majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags:
Jos