Yanzun Nan: Hafsoshin tsaro sun dira Hedkwatar yan sanda kan harin jirgin kasa

Yanzun Nan: Hafsoshin tsaro sun dira Hedkwatar yan sanda kan harin jirgin kasa

  • Hafsoshin tsaron ƙasar nan, yanzu haka sun shiga taron sirri a Hedkwatar dakarun tsaro dake birnin tarayya Abuja
  • Wata majiya ta ce shugabannin tsaron zasu tattauna kan Fasinjojin jirgin ƙasa da yan ta'adda suka yi garkuwa da su wata ɗaya kenan
  • A ranar Laraba da ta gabata yan bindigan suka saki Hotunan mutanen dake hannun su, maza da mata da kananan yara

Abuja - Babban hafsan tsaron ƙasar nan, Janar Lucky Irabor, Sufeta Janar na yan sandan ƙasa, Usman Alkali Baba, da sauran shugabannin tsaro yanzu haka sun shiga taron sirri a Hedkwatar tsaro, Abuja.

Wannan taron dake gudana na ɗaya daga cikin yunƙurin da shugabannin hukumomin tsaro ke yi don kubutar da Fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja, waɗan da aka sace wata ɗaya kenan.

Hafsoshin tsaron Najeriya.
Yanzun Nan: Hafsoshin tsaro sun dira Hedkwatar yan sanda kan harin jirgin kasa Hoto: emergencydigest.com
Asali: UGC

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa Hafsoshin tsaron na shan matsin lamba kan su tabbata sun kuɓutar da Fasinjojin kafin Eid-El-Fitr.

Kara karanta wannan

Ni 'dan Malamin addini ne, bana neman mulki, sai dai a rokeni in yi : Malami

Majiyar ta ƙara da cewa taron zai tattauna kan dabaru da kuma tsare-tsare na ɓangaren tsaro na babban zaɓen dake tafe duba da bayanan DSS na cewa yan ta'adda na shirin tada bama-bamai a wuraren ibada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene maƙasudin taron?

Majiyar ta ce:

"Abinda na sani shi ne shugabannin tsaron na taro ne kan yadda zasu kubutar da fasinjojin jirgin Kaduna, ina nufin waɗan da suka shiga hannun yan ta'adda. Da yuwuwar su duba tsaron babban zaɓe na gaba."

Bayanan da aka tattara a wurin taron ya nuna cewa an sanya alamar ba hanya a hanyar Asokoro da zata kaika zuwa Sakatariyar tarayya dake Abuja.

A ranar Laraban nan, yan ta'adda suka saki hotunan mutanen da suke tsare da su, waɗan da suka haɗa maza 17 da mata da kananan yara.

A wani labarin kuma An tsaurara matakan tsaro yayin da yan takarar PDP suka fara dira Sakatariya

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An tsaurara matakan tsaro yayin da yan takara suka fara dira Sakatariyar PDP

Jami'an tsaro sun mamaye Sakatariyar PDP dake Patakwal a jihar Ribas yayin da ake gab da fara tantance yan takara.

Yan sanda, DSS da sauran jami'an tsaro sun hana kowa shiga har sai ka gabatar da katin shaida ko da ɗan jarida ne kafin ka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262