Hukumar yan sanda ta damke dillalan makamai da bindigogin AK47 guda 57 a Jos
- Jami'an yan sanda sun samu gagarumar nasarar damke masu safarar makamai a garin Jos, birnin jihar Flato
- Daga cikin abubuwan da aka gano hannunsu akwai bindigogin Ak-47 guda hamsin da bakwai
- Kakakin hukumar yace an kaddamar da bincike don bibiyan abokar harkarsu da wadanda suke sayarwa makamai
Birnin tarayya Abuja - Hukumar yan sandan Najeriya ta damke masu safarar makamai hudu a Jos, jihar Plateau dauke da bindigogin AK47 guda hamsin da bakwai (57).
Kaakin hukumar, CSP Muyiwa Adejumobi, a jawabin da ya fitar ranar Alhamis yace matasa hudu masu matsakaicin shekaru kuma duka mazauna Jos na wannan harkar.
A cewarsa, an damke su ne sakamakon harin sirri da aka musu.
Yace:
"Jami'in rundunar FIB-IRT a harn sirri, sun damke wasu dilolin makamai hudu kuma sun kwato bindigar AK47 guda 57 da dinbin harsasai a Jos da wasu jihohi."
"Matasan sune Hamza Zakari (aka Hamzo) dan shekara 20, Abubakar Muhammed (aka Fancy) dan shekara 22, Umar Ibrahim dan shekara 25 da Muhammed Abdulkarim (aka Dan-Asabe) dan shekara 37, duka mazauna Jos."
Ya kara da cewa sun amsa laifin da ake zarginsu da shi kuma an gano suke dillancin makamai wa yan bindiga dake addaban al'ummar yankin.
A cewarsa, an kaddamar da bincike don bibiyan abokan harkarsu da wadanda suke sayarwa makamai.
Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP, sun ceto mutane 848 da aka sace
Hedikwatar tsaron Najeriya a ranar Alhamis ta sanar da cewa, a kalla mutane 848 da aka yi garkuwa da su ne sojoji suka kubutar a wani samame daban-daban a fadin kasar cikin makwanni uku da suka gabata.
Jaridar Punch ta rahoto cewa, da yake jawabi yayin wani taron manema labarai a Abuja, Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Janar Benard Onyeuko, ya kuma ce sojoji sun kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar ISWAP, Abubakar Dan-Buduma.
Ya kara da cewa an kuma kama masu kwarmato bayanai na ‘yan ta’addan a ayyuka daban-daban tsakanin 7 da 28 ga Afrilu, 2022.
Asali: Legit.ng