Yan bindiga sun kai hari gidan na hannun daman Buhari a jihar Kano
- Yan bindiga sun yi yunkurin fasawa cikin gidan babban jigon jam'iyyar APC dake Nasarawa jihar Kano
- Bayan rashin samun nasarar shiga gidan, Kakakin hukumar yan sanda yace sai sun binciko su
- Yan bindigan su daure masu gadin gidan yayinda akalla mutum daya cikinsu ya jikkata
Kano - Wasu yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun kai har gidan babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma na hannun daman Buhari, Farouk Adamu Aliyu.
Hanarabul Farouq wanda tsohon dan majalisar wakilai ne kuma mai takarar kujeran gwamnan jihar Jigawa a zaben 2023.
Yan bindiga, wanda aka ce kimanin su 10 sun kai hari gidansa dake layin Babura, karamar hukumar Nasarawa ta jihar misalin karfe 2 na dare, Daily Trust ta rahoto.
An tattaro cewa bayan rashin samun nasarar shiga cikin gidan, an sassari daya daga cikin masu gadin yayinda suka daure sauran.
Makwabta kuwa bayan jin hayaniyan dake gudana suka tuntubi hukumar yan sanda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwan lamarin yace da wuri suka tura jami'ai wajen.
Yan bindiga na ganin zuwan yan sanda suka gudu, a cewarsa.
Yace:
"Yayinda suka ga zuwan yan sanda, yan fashin suka gudu. Amma an kaddamar da bincike don damke dukkan wadanda suka gudu."
Dan siyasan kuwa ba ya gidan lokacin da aka kai hari, rahoton ya kara.
'Yan Hayar Gidana Su Na Yunƙurin Ganin Baya Na, Mai Gidan Haya Ya Fada Wa Kotu
A wani labarin kuwa, wani mai gidan haya, Abdulwaheed Akani, a ranar Juma’a ya bayyana gaban wata kotu a Ibadan inda ya kai karar ‘yan hayar gidansa, Oluwatosin Ogunbadejo da Blessing Olapade, inda ya ce su na yunkurin ganin bayansa, Premium Times ta ruwaito.
Yayin kai korafin ga kotu, Akani ya zargi Ogunbadejo (namiji) da Olapade (mace) da cutar da shi ta hanyar kin bin dokokin tsaron da aka shimfida a yankinsu.
Mai karar, wanda lauyansa, A.B. Bello ya jagorance shi gaban kotun ya ce a ranar 1 ga watan Oktoban 2021 ‘yan hayar guda biyu su ka amince da kasancewa masu bin doka.
Asali: Legit.ng