Fasto Ya Faɗa Wa Mabiyansa Tashin Duniya Ya Zo, Ya Ce Kowa Ya Biya N310,000 Don a Buɗe Masa Kofar Zuwa Aljanna
- Yan sanda sun gayyaci wani fasto wanda ake zargin ya yi wa'azin karshen duniya domin neman kudi daga mabiyansa
- Labarin da ya bazu a dandalin sada zumunta ya ce faston ya yi yemi kowanne mabiyinsa ya biya N310,000 kafin ya tafi da shi wani sansani a Ekiti
- Wani cikin mabiya faston ya ce faston ya fada musu a can sansanin ne kofar zuwa sama za ta bude domin su tashi zuwa aljanna a yayin da karshen duniyan ke zuwa
Ekiti - Yan sanda a Jihar Ekiti sun gayyaci wani fasto da ake zargin cewa ya yi wa mabiyansa wa'azin cewa karshen duniya ta zo kuma su tara masa kudade don ya bude musu kofar zuwa aljanna, rahoton Premium Times.
Yan sandan sun ce faston ya bukaci mambobinsa su koma wani sansani a Araromi-Ugbesi a Omuo-Oke-Ekiti a karamar hukumar Ekiti ta Gabas na jihar 'domin su shirya wa karshen duniya.'
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai magana da yawn yan sandan jiha, ASP Sunday Abutu, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Ado Ekiti a ranar Laraba.
A cewar kakakin yan sandan, mun gayyaci faston, Nuah Abraham na Cocin Christ High Commission Ministry, wanda aka fi sani da Royal Christ Assembly, Jihar Kaduna, Daily Nigerian ta rahoto.
Ya ce an gayyaci faston ne kan zargin "ya bukaci mambobinsa su bashi N310,000 domin ya taya su shirin zuwan karshen duniya."
Ya ce an gayyaci faston domin ya yi karin bayani kan ikirarin da ya bazu a dandalin sada zumunta.
Ana zargin Abraham ya bukaci kowanne mamba a cocinsa su koma wani sansani a Omuo-Ekiti daga Jihar Kaduna yana mai cewa a can ne tashin duniyan zai fara.
Wani cikin mabiyan faston ya ce ya bukaci duk mai son a bude masa kofar aljanna ya biya N310,000
Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta rahoto cewa wata majiya, wacceita ma tana zuwa cocin Abraham, ta tabbatarwa manema laabarai cea da farko faston ya koma Ekiti a 2021 daga tsohon cocinsa da ke Kaduna.
"Daga baya ya koma Kaduna a watan Afrilu ya bukaci kowanne mambansa a cocin ya biya shi N310,000 kafin ya yarda su bi shi zuwa Araromi a Omuo-Oke-Ekiti a Jihar Ekiti," a cewar mabiyin.
Majiyar, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya kara da cewa faston ya yi hudubar cewa a can sansanin ne 'kofar sama za ta bude musu su tashi zuwa aljanna.'
Asali: Legit.ng