Gwamnati ta kashe N4.6bn wajen horar da matasan N-Power kimanin 13,000: Hajiya Sadiya

Gwamnati ta kashe N4.6bn wajen horar da matasan N-Power kimanin 13,000: Hajiya Sadiya

  • Gwanatin tarayya ta kammala shirin horas da matasa marasa digiro zango na uku a jihar Legas
  • Ministar tallafi ta bayyaa cewa an kashe sama da bilyan hudu da rabi wajen horas da mutum 12,981
  • Shugaba Buhari ya bada izinin fadada tsarin NSIP ta yadda za ta shiga kowani lungu da sakon kasar nan, cewar Hajiya Farouq

Legas - Ma'aikatar tallafi, walwala da jin dadin al'umma, a ranar Talata, ta bayyana cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta kashe N4.6billion don horas da matasan N-Power Batch C guda 12,981.

Ministar ma'aikatar, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ce ta bayyana hakan a bikin yaye matasa 62 da aka koyawa gyaran waya a Legas, rahoton Leadership.

Minista Sadiya Umar Farouq, tace an yi amfani da kudin ne wajen horas da su, basu kayan aiki, da kudin tukuwicin da ake basu a wata.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Hajiya Sadiya
Gwamnati ta kashe N4.6bn waje horar da matasan N-Power kimanin 13,000: Hajiya Sadiya Hoto: @sadiya_farouq
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hajiya Farouq, wacce ta samu wakilcin Diraktar HR na ma'aikatar tace manufar wannan shiri shine rage rashin aikin yi bisa kudirin Shugaban kasa na rage talauci.

Tace:

"An fadada shirin masu digiri da marasa digiri na shirin N-Power don samawa marasa aiki 12,981 a Legas karkashin Batch C, bayan samun nasarar kammala horas da Batch A da B mutum 16,694."
"Karkashin NSIP, gwamnatin tarayya ta zuba kudi N4.6 billion wajen horas da matasan, basu kayan aiki da biyan kudin albashin matasan Batch C."

Farouq ya kara da cewa Shugaba Buhari ya bada izinin sauya tsarin NSIP ta yadda za ta shiga kowani lungu da sakon kasar nan.

Gwamnati za ta baiwa matasa guda 98,000 bashin kudin N50,000 zuwa N300,000: Sadiya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala shirin baiwa yan Najeriya mutum 98,000 bashi maras kudin ruwa cikin tsarin Government Enterprise and Empowerment Programme (GEEP) 2.0.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Majalisa Ta Nemi Ministar Buhari Ta Sauka Daga Mukaminta, Ta Faɗi Dalili

Ministar walwala, tallafi da jin dadin mutane, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan a jawabin da mai magana da yawunta, Nneka Anibeze, ta fitar ranar Laraba, rahoton NAN.

Hajiya Sadiya ta ce wadanda aka zaba zasu samu bashin kudi N50,000 zuwa N300,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida