Babu gwamnatin da ta yiwa yan kasuwa kokari kamar gwamnati na, Shugaba Buhari

Babu gwamnatin da ta yiwa yan kasuwa kokari kamar gwamnati na, Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa ya sha ruwa da jiga-jigan yan kasuwa masu aiki a kamfanin attajiri Aliko Dangote
  • Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa na baiwa yan kasuwa goyon baya matuka
  • Buhari ya bukaci ‘yan kasuwa da su saka hannun jari a fannoni daban-daban da za su kawo ci gaban tattalin arzikin kasar nan

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yan kasuwa sun fi samun saukin kasuwancinsu a Najeriya yanzu fiye da shekarun baya.

A bisa jawabin da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, Shugaba Buhari ya yi jawabin ne lokacin da ya karbi bakuncin yan kasuwa zaman shan ruwa a fadar shugaban kasa ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

Shugaban kasa yace gwamnatinsa ta yi namijin kokari wajen inganta kasuwanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa

Shugaban kasa ya yi kira ga yan kasuwan su bada nasu gudunmuwar wajen kawar da talauci da samawa matasa aikin yi.

A 2020, Najeriya ce ta 131 a jeringiyar kasashen da aka fi saukin kasuwanci a duniya bisa rahoton Bankin Duniya.

Buhari yace:

"Babu gwamnatin da tayi kokari wajen saukaka kasuwanci ga manyan yan kasuwa da kanana."
"Rahoton saukin kasuwanci da aka yarda da shi a duniya ya tabbatar da cewa ana samun saukin kasuwancin a kasar nan fiye da kowani gwamnati a tarihi."
"Hakazalika muna kyautata zaton yan kasuwan masu zaman kansu zasu taimakawajen inganta tattalin arziki da samawa matasa ayyukan yi."

Shugaba Buhari
Babu gwamnatin da ta yiwa yan kasuwa kokari kamar gwamnati na, Shugaba Buhari Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

A ranar Juma’a, 22 ga watan Afrilu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci ‘yan kasuwa da su rika amfani da dabaru don habaka fannonin tattalin arziki, tare da yin tasiri mai tsawo wajen samar da ayyukan yi da rage radadin talauci.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar sukar gwamnatin Buhari da Rarara ya yi

Ya ba da wannan sahwara ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban rukunin masana'antun Dangote, Aliko Dangote da mambobin rukunin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban ya ce kalubalen harkokin sufuri da makamashi za su ci gaba da jan hankalin jama’a a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng