Wani Bam ya fashe bayan Sallar Tarawihi a gidan giya a jihar Yobe

Wani Bam ya fashe bayan Sallar Tarawihi a gidan giya a jihar Yobe

  • Wani abun fashewa ya yi ajalin mutum ɗaya, wasu kusan Bakwai sun jikkata a garin Gashua, hedkwatar karamar hukumar Bade a Yobe
  • Wani mai shago a kusa da wurin da abun ya faru, Abdu Sherrif, ya ce suna cikin Sallar Isha'i suka jiyo tashin abun fashewar
  • Shugaban ƙaramar hukumar Bade, Sanda Kara Bade, ya ce tuni aka ɗauke waɗan da abun ya shafa domin ba su kulawa a Asibiti

Yobe - Mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa wasu kusan Bakwai sun jikkata sakamakon fashewar wani abun fashewa a wani gidan Giya da ake kira 'Gidan Amarya,' a jihar Yobe.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a garin Gashua, Hedkwatar karamar hukumar Bade, a jihar dake arewa maso gabashin Najeriya.

Mazauna garin sun bayyana cewa an jiyo ƙarar fashewar abun a dukkan sassan Gashua da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Lahadi bayan sallan Tarawihi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam ya ƙara fashewa a babban birnin jihar Arewa, ya shafi mutane da dama

Taswirar jihar Yobe
Wani Bam ya fashe bayan Sallar Tarawihi a gisan giya a jihar Yobe Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wani mai shago a kusa da gidan giyan, Abdu Sherrif, ya ce mutane da yawa sun yi takan su domin neman wurin tsira da rayuwarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sherrif ya ce:

"Na ji ƙarar fashewar muna tsaka da sallar Isha'i, kuma muna sallame wa muka tsere zuwa gidajen mu domin ɓuya."
"Bayan wani lokaci sai labari ya zo mana cewa wani abu ne ya fashe a ɗakin giya a wani yankin dake maƙwaftaka da mu."

Hukumomin karamar hukumar sun tabbatar da lamarin

Shugaban ƙaramar hukumar Bade, Sanda Kara Bade, ya ce gwamnatinsa ta tura jami'an tsaro zuwa wurin kuma ya ba da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin fashewar.

Ya ce tuni aka ɗauke mutanen da suka jikkata sanadiyyar lamarin zuwa Asibitin gwamnati don kula da lafiyar su.

Babu cikakken bayani kan ƙungiyar da ta ɗauki nauyin wannan harin na Bam, wanda ya faru kwanaki biyu bayan mayaƙan Boko Haram sun yanka mutum 10 a 'Kwari' wani wuri a Geidam, jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Fitattun Attajirai biyu sun lale miliyan N200m zasu siyawa mutum biyu Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a APC

A makon da ya gabata, kungiyar ta'addanci ISWAP ta bayyana cewa ita ta ɗauki nauyin kai hari Mashaya guda biyu a jihar Taraba.

A wani labarin na daban kuma Matar tsohon gwamnan jihar Anambra a Najeriya ta rigamu gidan gaskiya

Matar tsohon gwamnan Farko a mulkin farar hula a jihar Anambra, Misis Christiana Njideka Ezeife, ta kwanta dama.

Gwamnan jihar na yanzu, Farfesa Charles Soludo, shi ya tabbatar da haka, ya kuma kai ziyarar ta'aziyya har gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: