Duniya kenan: ‘Dan Majalisar Tarayya ya rasu kwatsam, ana shirin fara lissafin 2023

Duniya kenan: ‘Dan Majalisar Tarayya ya rasu kwatsam, ana shirin fara lissafin 2023

  • An tabbatar da mutuwar ‘Dan majalisar tarayya daga yankin Akwa Ibom, Nse Bassey Ekpenyong
  • Har a makon da ya gabata, Hon. Nse Ekpenyong ne mai wakiltar mazabar Oro a majalisar wakilai
  • Marigayin ya rike kujerar majalisar dokoki kafin zamansa ‘dan majalisar tarayya bayan zaben 2015

Akwa Ibom - A ranar Lahadi, 24 ga watan Afrilu 2022 mu ka samu labarin mutuwar daya daga cikin ‘yan majalisar wakilan tarayya da ke Najeriya, Nse Ekpenyong.

Ana tunanin Honarabul Nse Ekpenyong mai shekara 58 a Duniya ya rasu ne a ranar Asabar. Jaridar Premium Times ce ta fitar da wannan rahoton a jiya.

Kafin rasuwarsa, Hon. Nse Ekpenyong shi ne mai wakiltar mazabar Oron a majalisar wakilan tarayya a karkashin babbar jam’iyyar hamayya watau PDP.

Kara karanta wannan

Sarkin Oyo ya hango mutuwarsa, ya fada mana cewa magabatansa sun yi kira - Hadimarsa

Jaridar ta ce shugaban karamar hukumar Mbo a jihar Akwa Ibom, Hon. Asuqwo Eyo ya tabbatar mata da labarin mutuwar wannan ‘dan siyasa da ake ji da shi.

Asuqwo Eyo ya ce Hon. Nse Ekpenyong wanda ya fito daga yankinsa bai fama da wata rashin lafiya, farat daya aka ji kwatsam mutuwa tayi halinta a kan shi.

Saura kusan shekara daya kenan ‘dan siyasar ya kammala wa’adinsa na biyu a matsayin ‘dan majalisar tarayya. A 2015 Ekpenyong ya tafi majalisar wakilai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majalisar Tarayya
'Yan majalisar wakilan tarayya Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Tarihin siyasar Marigayin a PDP

Kafin zamansa ‘dan majalisa, Marigayin ya wakilci mazabarsa a majalisar dokoki na jihar Akwa Ibom, sannan ya taba zama mataimakin shugaban PDP na jiha.

Rahoton ya ce Ekpenyong ya rike Darektan wani kamfani da ake kira Investment Trust Co Nigeria. Daga baya ya zama shugaban kamfanin Brule Integrated Nig. Ltd.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori tsohon kakakin majalisa Dogara daga majalisar wakilai

Bisa al’ada shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila zai bada sanarwar rasuwarsa, daga nan sai hukumar INEC ta shirya yin zabe na cike gurbinsa.

Shari'ar EFCC da Ekpenyong

Legit.ng Hausa ta fahimci Nse Bassey Ekpenyong ya yi karatun sakandare ne a Oti-Obor, kafin ya samu shaidar karamar difloma a wata makaranta da ke jihar Abia.

A shekarar 2017 aka yi ta shari’a da shi a babban kotun tarayya mai zama a garin Uyo, hukumar EFCC ta na zargin ‘dan siyasar yana amfani da shaidar karatun bogi.

Rikicin gidan PDP

An ji cewa kakakin kungiyar NEF ya yi karin haske a kan dambarwar da aka shiga game da takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP tsakanin ‘yan siyasan Arewa.

Dr. Hakeem Baba Ahmed a madadin kungiyar dattawan ya ce tsaida wanda za su yi wa jam’iyyar PDP takara a zaben 2023 aikin ‘ya 'an jam’iyya ne ba na dattawa ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna kuma Aminin Buhari ya shirya tsaf domin takarar Shugaban kasa a APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel