Duk da tarin dukiyarta, Biloniya Folorunso ta yi kira ga mata da su yi wa mazansu biyayya
- Biloniyan nan 'yar Najeriya, Folorunso Alakija ta yi magana a kan bukatar mata su dinga girmama mazajensu a gidajensu na aure
- Fitacciyar 'yar kasuwar, ta kara da cewa, kada maza su zubar da kimarsu, akwai bukatar su ma su nuna halin dattaku ga matansu
- Mutanen da suka yi tsokaci ga bidiyon wa'azinta a Facebook sun bayyana ra'ayoyi mabambamta, yayin da wasu suka kawo dalilai da ke kalubalantar hakan
Legas - Fitacciyar 'yar kasuwar nan ta Najeriya, Folorunso Alakija, tayi wa'azi a kan bukatar mata su dinga biyayya ga mazajensu.
Yayin da ta yanko daga littafin Ephesians na Injila, matar da tafi kowacce mace kudi a Najeriya ta karfafa zanceta, inda ta kara da cewa, kada maza su yi amfani da damar biyyayar da ake musu wurin muzgunawa.
Maza su girmama matansu
Yayin da karantowa daga littafin Ephesians na Injila aya ta biyar, ta ce maza da dama basa son amfani da bangaren da ya umarci ma'aurata da su girmama junansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani bangare na wallafarta na nuni da: "Yayin da akwai hujjoji da dama a Injila a kan yadda ya kamata mace tayi rayuwar aure, haka zalika akwai hanyoyi da ke jagorantar maza a kan yadda ya kamata su kula da matansu. Bayan duba da nazari da hakan, wajibi ne maza su bada so, kula da yabawa matayensu."
'Yan Najeriya sun yi martani
Ga wasu daga cikin tsokacin wallafar ta:
Mmaphuti Fortunate Matshela ta ce: "Amin. Hakan ya yi kyau kuma abun lura ne. Muna godiya da wannan fadakarwa mai cike da ilimi. Ubangiji ya kara daukaka ki Folorunso Alakija."
N'da Yao Cyril Kimenan ya kalubanci hakan:
"Na yarda da wa'azin ki dari bisa dari, amma maganar gaskiya wacce irin "biyayya" za mu iya yi. Misali: idan ma'auratan suka samu sabani a wani abu, ta ya kalmar "biyayya" za tayi amfani wurin magance sabanin?"
Jackson Mpala ya ce: "Malama ki fara karanta abunda littafin Injilan ya kunsa, kafin ki hau wa'azin. Ya kamata ki fahimci kalmomin."
2022: Manyan biloniyoyi mata 10 na duniya, sunayensu, kasa da adadin dukiya
A wani labari na daban, daga cikin biloniyoyi 2,668 na shekarar 2022 da Forbes ta fitar, mata kadan aka samu. An samu 327, kasa da 328 na shekarar da ta gabata (har da matan da dukiyarsu ta hada da ta mazansu, 'ya'ya ko 'yan uwa) suna da jimillar $1.56 tiriliyan fiye da ta shekarar da ta gabata da ta kai $1.53 tiriliyan.
Da yawa daga cikin hamshakan matan nan, 226 daga cikinsu sun samu dukiyarsu ne ta hanyar gado. Sun hada da mata uku na farko a duniya masu tarin arziki. Akwai L'Oreal wacce ta gaji Francoise Bettencourt Meyers, Walmart, magajiyar Alice Walton da Julia Koch, wacce ta gaji masana'antun Koch bayan mutuwar mijinta David Koch a shekarar 2019.
“Na Rasa Sukuni”: Dan Najeriya Ya Koka a Bidiyo, Ya ce Matar Da Ya Aura Ya Kai Turai Tana Sharholiya Da Maza
Asali: Legit.ng