'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kisan Mutum 10 Da Boko Haram Suka Yi a Geidam
- Rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe ta tabbatar da halaka mutane 10 tare da raunana mutane da dama da wasu ‘yan Boko Haram suka yi a garin Geidam
- Lamarin ya auku ne a ranar Laraba kamar yadda kakakin rundunar, Dungus Abdulkarim ya tabbatar wa manema labarai ranar Asabar a Damaturu
- Kakakin ya ce tuni tsaro ya dawo yankin bayan tura jami’an tsaro su na sintiri don gudun kara aukuwar farmakin nan gaba
Jihar Yobe - Rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe ta tabbatar da batun kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yi wa mutane 10 yayin da su ka raunana wasu da dama, The Nation ta ruwaito.
A ranar Laraba mummunan lamarin ya auku kamar yadda kakakin rundunar, Dungus Abdulkarin ya shaida wa NAN a Damaturu ranar Asabar.
Ya ce ‘yan ta’addan sun isa a babura ne yayin da su ka zagaye rukunin gidajen malaman makarantun gwamnatin yankin.
Rundunar ‘yan sanda ta jajantawa jama’an Geidam, In Ji Abdulkarim
Ya ci gaba da cewa:
“Yanzu haka tsaro ya dawo yankin don mutane sun ci gaba da zirga-zirgarsu yayin da aka tura jami’an tsaro yankin su na sintiri don gudun harin ya maimaita kansa.”
Abdulkarim ya ce rundunar ‘yan sanda ta jajantawa mutanen Geidam akan harin kuma ta bukaci mutane su yi gaggawar sanar da jami’an tsaro idan sun kula da wani abin zargi.
'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed
A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.
Dakarun hadin gwiwa sun yi gagarumin nasara: Sun kashe kwamandojin ISWAP 10 da mayaka 100 a tafkin Chadi
Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.
Asali: Legit.ng