Rundunar yan sanda ta fallasa sunaye da Hotunan mutum 12 da take nema ruwa a jallo kan hannu a ta'addanci
- Hukumar yan sandan ƙasar nan ta bayyana sunaye da hotunan wasu mutum 12 da take nema ruwa a jallo kan zargin ta'addanci
- Kakakin yan sanda, Muyiwa Adejobi, a wata sanarwa ya ce ana zargin mutanen da aikata manyan laifukan ta'addanci a Anambra
- Ya kuma yi kira ga al'umma su taimaka wa dakarun yan sanda da bayanai domin doka ta yi aiki kan waɗan da ake zargin
Abuja - Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana sunayen wasu mutum 12 da take nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a kai hare-hare ƙaramar hukumar Awka ta arewa, jihar Anambra.
Kakakin yan sanda, Muyiwa Adejobi, a wata sanarwa, ya ce mutanen 12 da ake zargi sun aikata laifukan haɗa baki, kisan kai, ta'addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami asiri da kuma mallakar bindigu ba bisa ƙa'ida ba.
Kakakin yan sandan ya ambato sunayen mutane da suka haɗa da, Edward Okoye, Donatus Okeke, Onyemazi Ngini, Onyebuchi Okoye, Nonso Eboh, da Chukwuka Onyibor.
Sauran sune; Chukwujekwu Anaekeokwu, Chuka Ilodigwe, Chinedu Okoye, Nonso Obinna, Cosmos Okonkwo da kuma Chukwujekwu Okoye.
Kotu ta ba da umarnim kame mutunen
Wani sashin ranarwan da rundunar yan sandan ta sanya a shafinta na Twitter ta ce:
"Tun da farko, hukumar yan sanda ta samu nasarar samun umarnin Kotu na ayyana neman waɗan da ake zargi, baki ɗaya mazan ƙabilar Ibo dake tsakanin shekaru 25-55, mazauna Isu-Aniocha, yankin Awka ta arewa a Anambra."
Hukumar yan sandan ta kuma bayyana irin ta'asar da mutane suka aikata, wanda ya haɗa kai hari Ofisoshin yan sanda, da kashe Jami'ai da dai sauran su.
Kazalika hukumar yan sanda ta roki al'umma su taimaka da, "Bayanai sirri da za su taimaka wajen kame mutanen da kuma tabbatar da doka ta yi aiki a kan su."
A wani labarin kuma Wasu yan bindiga sun saki sabon Bidiyo, sun yi barazanar hana zaɓen 2023 dake tafe
Bidiyon mai tsawon mintuna biyu da dakika 55, wanda aka ɗauka a cikin ƙungurmin daji, ɗaya daga cikin yan bindigan ya ce abin da ya sa suka ja daga shi ne tsare shugaban yan awaren kafa ƙasar Biafara (IPOB), Nnamdi Kanu.
Dan bindigan da ya yi maganan, ya yi iƙirarin cewa babu wanda ke ɗaukar nauyin su, inda ya jaddada cewa, " Duk mutumin da ya jaraba yunkurin gudanar da zaɓe zai mutu."
Asali: Legit.ng