Da duminsa: An damke wani mai hadawa yan ta'addan IPOB Bam a Kudu maso gabas
- Jami'an yan sanda a kudu maso gabas sun cika hannu da mai hadawa yan ta'addan IPOB bama-bamai
- A sansanin da suke hada bama-baman, an bankado garin bindiga da sinadaren da ake amfani wajen hada bam
- Yan ta'addan IPOB sun addabi al'ummar yankin kudu maso gabas musamman jihar Imo
Hukumar yan sandan jihar Imo a ranar Juma'a ta damke wani mutumi mai suna, Simeon Onigbo, wanda ake zargin mai hada Bam ne wa yan awaren Indigenous People of Biafra, IPOB da suke amfani wajen kai hare-hare ofishohin yan sanda da ofishohin gwamnati a jihar.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya bayyana hakan ga manema labarai a Owerri, rahoton Vanguard.
Yace a ranar Laraba ta gano sansanin hada bama-bamai a Uba Umuaka, karamar hukumar Njaba dake jihar Imo bayan samun bayanai na leken asiri.
A cewarsa:
"Sakamakon bayanan kwakwaf da muka samu ranar 20/4/2022 misalin karfe 1700hrs, na inda yan awaren IPOB ke hada bama-bamai da ake amfani da su wajen kai hari ofishohin yan sanda da dukiyar gwamnati a jihar."
"A harin da yan sanda suka kai wajen, an damke wani dan shekara 50, Simeon Onigbo."
"Yayin amsa tambayoyi, ya tabbatar da cewa shi ke hadawa yan ta'addan Bam din da suke amfani wajen kaiwa yan sanda hari a yankin.'
Kaakin yan sandan ya kara da cewa mutumin ya bayyana wa hukuma sunayen wadanda suke hada Bam din tare a jihar Imo da wasu jihohi.
Ga jerin abubuwan da suka tarar a wajen:
Bam daya da aka kammala hadawa
Pipe 58
Guduma 1
Rabin buhun sinadarin hada Bam Potassium Nitrate KNO3
Sinadrin Sulpur
Fam 40 na kasa
Fam 58 na jar kasa
Fam 30 na garin bindiga
Rabin buhun gawayi
Baturan babur 30
Roduna
Rundunar yan sanda ta fallasa sunaye da Hotunan mutum 12 da take nema ruwa a jallo kan hannu a ta'addanci
Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana sunayen wasu mutum 12 da take nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a kai hare-hare ƙaramar hukumar Awka ta arewa, jihar Anambra.
Kakakin yan sanda, Muyiwa Adejobi, a wata sanarwa, ya ce mutanen 12 da ake zargi sun aikata laifukan haɗa baki, kisan kai, ta'addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami asiri da kuma mallakar bindigu ba bisa ƙa'ida ba.
Asali: Legit.ng