Sabon nadi: Buhari ya nada mai taimaka masa kan samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya

Sabon nadi: Buhari ya nada mai taimaka masa kan samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Misis Matilda Mmegwa a matsayin babbar mai bashi shawara kan samar da aikin yi
  • Mmegwa wacce ta rike mukamai daban-daban a gida da waje za ta yi aiki ne a karkashin ministan kwadago da daukar ma’aikata
  • Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ne ya sanar da wannan sabon nadin a cikin wata sanarwa da ya saki a yau Alhamis

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Misis Matilda Mmegwa a matsayin babbar mai ba shugaban kasa shawara kan dauka da samar da aikin yi.

Sabuwar hadimar shugaban kasar wacce ta rike mukamai daban-daban a kamfanoni masu zaman kansu a Kanada da kungiyoyin kasa da kasa, za ta yi aiki ne a karkashin shugabancin ministan kwadago da daukar ma’aikata.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin watsa labarai, Mista Femi Adesina, ya saki a ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu, TVC News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kada kowa yazo da waya: Aisha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu

Sabon nadi: Buhari ya nada mai taimaka masa kan samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya
Sabon nadi: Buhari ya nada mai taimaka masa kan samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya
Asali: Facebook

Adesina ya ce Misis Mmegwa da aka nada a mukamin tana da gogewa na sama da shekaru 30 a bangaren dabarun shugabanci, gudanar da harkokin kamfanoni, hada kan jama'a da ci gaban tattalin arziki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kasance babbar mai gabatarwa ta kasa da kasa, kuma ta kasance jagorar masu jawabi a taron kungiyar CAPAM a kasar Tanzania a 2009.

Misis Mmegwa ta yi aiki a matsayin babbar mai ba da shawara da dabaru a shirin GASIP, wani shiri na asusun ci gaban aikin gona na Duniya (IFAD) da gwamnatin Ghana.

Ta mallaki digiri a ‘Industrial Chemistry’, ta yi kwas na musamman a matsayin babbar akawu a Najeriya da Kanada, ta mallaki digiri na biyu a bangaren ‘Strategy and Corporate Governance’, rahoton Premium Times.

Shugaba Buhari ya gana da hafsoshin tsaro, ministoci kan batun tsaron Najeriya

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Abin da ya sa aka ga Buhari ya yafewa tsofaffin Gwamnonin da ke kurkuku

A wani labari, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar wata ganawa da wasu ministoci da shugabannin hukumomin tsaro a fadarsa da ke Abuja.

Taron wanda aka fara shi da misalin karfe 10 na safe, ya biyo bayan shawarwarin da majalisar dokokin kasar ta bayar ne kan duba lamarin rashin tsaro a fadin kasar.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd.) sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng