El-Rufai Bada Miliyan 18 Ga Iyalan Mutum 9 Da Ƴan Uwansu Suka Mutu a Harin Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Abuja

El-Rufai Bada Miliyan 18 Ga Iyalan Mutum 9 Da Ƴan Uwansu Suka Mutu a Harin Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Abuja

  • Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da bayar da Naira miliyan 18 ga ‘yan uwan wadanda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya afka mawa
  • Sakataren hukumar Bada da Agajin Gaggawa na Jihar Kaduna, KADSEMA, Muhammed Mukaddis, ya bayyana hakan a ranar Laraba
  • A cewarsa, gwamnan ya amince da bayar da N250,000 ga kowa cikin mutane 22 da suka samu miyagun raunuka sakamakon harin jirgin kasan

Kaduna - Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna, KADSEMA, Muhammed Mukaddas ya bayyana yadda gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da bayar da Naira Miliyan 18 ga mutane 9 wadanda mummunan harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya ritsa da su.

Mukaddas ya bayyana hakan ne a ranar Laraba inda ya ce a ranar 19 ga watan Afirilu gwamnatin ta amince da bayar da Naira Miliyan 2 ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta dalilin harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Zulum ya yi rabon buhuhunan hatsi, kudi da atamfa ga mutum 100,000 a cikin garin Maiduguri da Jere

Harin Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna: El-Rufai Ya Bai Wa Iyalan Mutum 9 da Harin Ya Ritsa Da Su N18m
El-Rufai Ya Bai Wa Iyalan Mutum 9 Da Harin Jirgin Kasan Kaduna Ya Ritsa Da Su N18m. Hoto: Gwamnatin Kaduna.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mukaddas ya ce gwamnan ya amince da biyan mutane 22 da suka raunana dalilin harin, inda ya ce za a ba ko wannensu N250,000.

Sakataren KADSEMA ya ce ba an biya su kudaden don biyansu asarorin da suka tafka ba ne, an bayar ne don tallafa musu.

Mukaddas ya ce amfanin hukumarsu kenan, kawo taimakon gaggawa idan bukatar hakan ta taso

A cewarsa, kamar yadda Daily Nigerian ta nuna, amfanin hukumar tasu ne kawo tallafin gaggawa yayin da wani ibtila’i ya auku ko kuma bukatar hakan ta taso.

A cewar Mukaddas:

“An kira mutane 369 don a tallafa musu wurin kwantar musu da hankali, mutane 264 ne suka amince da tallafin kuma har an ba su.”

Ya bayyana yadda aka sanar da hukumar wacce cikin gaggawa aka sanar da manyan ma’aikatan gwamnati da duk wadanda suka dace su sani, daga nan suka hada gwiwa wurin taimako tare da jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Al-mundahana: EFCC ta Tsare Ɗan Tsohon Gwamnan Nasarawa kan wasu Kudade N130m

Ya ci gaba da cewa:

“Mun samar da motoci don kwashe mutane daga wurin, kafin mu isa sojoji sun fara kwashe mutane, daga nan ne muka fara kwashe gawawwaki da kuma wadanda suka raunana yayin da muka dauki mutum daya wanda ya gudu daga hannun masu garkuwa da mutane.”

Ya ce sun hada kai da ma’aikatar lafiya wurin kulawa da marasa lafiyan

Kamar yada ya ce:

“Mun ajiye gawawwakin asibitin 44 NARH, yayin da muka kai wasu asibitin St. Gerald don a duba lafiyarsu. Sannan muka samar da hanyar tattaunawa da ‘yan uwan wadanda suka bata don samun bayanai akansu.”

Mukaddas ya ce hukumar ta hada kai da ma’aikatar lafiya don biyan kudaden asibiti tare da tabbatar da lafiyar magungunan da aka kai Asibitin Sojoji na 44 da St. Gerald.

Idan ba a manta ba a ranar 28 ga watan Maris aka kai wa fasinjojin jirgin kasa farmaki a Katari da ke Jihar Kaduna inda ‘yan ta’adda suka halaka fiye da fasinjoji 8 yayin da wasu suka raunana, sannan suka sace mutane da dama.

Kara karanta wannan

Ku kawo fansa ko mu kashe sauran: 'Yan bindiga sun hallaka mutum 3 da suka sace a Kaduna

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel