Ku Ba Mu N200m Cikin Kuɗin Tallafin Man Fetur, Mu Koma Aji: ASUU Ta Roƙi Gwamnatin Buhari
- Yayin da Kungiyar Malamai na jami’o’in Najeriya, ASUU ke kokarin sansantawa da Gwamnatin Tarayya, har yanzu ta tsaya akan bukatun kungiyar
- Hakan ya biyo bayan yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza biya mata bukatunta, wanda yanzu haka dalibai suna zaman jira duk da babu ranar komawa
- Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osedeke ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan lalubowa cikin asusun tallafin mai wurin cika musu bukatar kungiyar
Shugaban Kungiyar malaman jami’o’i masu koyarwa, ASUU, Farfesa Emmanuel Osedeke ya ce gwamnatin tarayya har yanzu tana nuna halin ko-in-kula akan yajin aikin ASUU wanda hakan ya sa daliban jami’o’in Gwamnatin Najeriya suke zaune a gidajensu, rahoton The Punch.
A cewarsa, gwamnati ta kawo mafita akan kudin tallafin man fetur da kasafin Naira tiriliyan 4 amma kuma har yanzu bata ce komai ba akan ilimin jami’o’inta.
Farfesa Osodeke ya ce Naira biliyan 200 gwamnati za ta cire daga kudin kasafin tallafin man fetur, Naira Tiriliyan 4, sannan ta samu rarar Naira Tiriliyan 3.8 wurin kawo karshen matsalolin jami’o’i, Channels Television ta rahoto.
Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta nuna muhimmancin ilimi akan komai
Osedeke ya kara da kira ga Gwamnatin Tarayya aman nuna muhimmancin ilimi akan tallafin kudin man fetur, wanda ya ce shi ne ya fi cancanta a fi darajawa.
A cewarsa, Jami’o’in Najeriya za su iya samar da matatun man fetur cikin shekaru uku, kuma hakan daya ne daga cikin hanyoyin kawo karshen asarorin da ake samu a tallafi.
Farfesa Osedeke ya ci gaba da cewa:
“Abin akwai ban mamaki ace wai Gwamnati ba za ta iya tara Naira biliyan 200 duk shekara wurin inganta jami’o’i ba.
2023: A Manta Da Batun Zaɓe Bayan Saukan Buhari, a Kafa Gwamnatin Wucin Gadi Da Za Ta Saita Najeriya, Dattijon Ƙasa Ya Bada Shawara
“Amma kuma Gwamnatin tana iya tara Naira Tiriliyan 4 na tallafin man fetur. Tsakanin kudin tallafin man fetur da kuma ilimin Najeriya, wanne ya fi muhimmanci?
“Kuna iya kashe Naira Biliyan 228 don ciyar da daliban makarantun firamare da na sakandare. Amma ba za ku iya amfani da kudi wurin gyara jami’o’i ba. Wannan ita ce babbar matsala.
“Idan aka cire Naira miliyan 200 cikin Naira Tiriliyan 4, don tallafa wa jami’o’i, akwai ragowar Naira Tiriliyan 3.8 na kudin tallafin man fetur.”
Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Bar Titunan Abuja Ba Har Sai An Buɗe Makarantu, 'Kungiyar NANS
A bangare guda, Kungiyar Daliban Najeriya, NANS, a ranar Litinin ta cigaba da zanga-zangar ta na neman ganin an kawo karshen yakin aikin da kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ke yi.
Da ya ke magana a yayin zanga-zangar a Abuja, shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya ce daliban a shirye suke su fito su mamaye manyan titunan Abuja, rahoton The Punch.
Ya kara da cewa daliban sun gaji kuma ba za su fasa abin da suka fara ba har zai an bude dukkan jami'o'i a kasar.
Asali: Legit.ng