Yanzu-yanzu: N100m muke sayar da Fom din takarar kujerar shugaban kasa, Jam'iyyar APC
- Fiye da abokiyar hamayyarta sau ninki biyu da rabi, APC ta ce N100m za ta sayar da Fam din takara kujerar shugaban kasa
- Akalla mutum goma sha biyar suka alanta niyyar gajen shugaba Buhari karkarshin jam'iyyar APC
- Za'a gudanar na kujeran shugaban kasa mako guda bayan gudanar da na gwamnoni
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yanke shawara kan farashin da zata sayar da fam ga duk wadanda ke son takarar kujerar shugaban kasa a 2023 karkashin lemarta.
APC ta ce naira milyan dari kowani dan takara zai biya don yankan Fom.
A cikin kudi N30m na takarar ayyana niyya ne, N70m kuma kudin takardar neman kujeran ne.
Wannan na cikin abubuwan da aka yanke shawara kansu a taron majalisar zartaswar jam'iyyar da aka yi ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.
Za'a fara sayar da Fam din daga ranar 22 ga Afrilu, 2022.
Na gwamna kuwa, za'a sayar da Fam din N50m yayinda masu neman kujerar Sanata zasu kashe N20m.
APC har ila yau ta ce N10m za ta sayar da Fam ga masu neman kujerar yan majalisar wakilai sannan masu neman takarar kujerar majalisar jiha N2m.
Ga jerin farashin nan:
Jerin sunayen wadanda suka ayyana niyyar takara karkashin jam'iyyar APC:
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Prof Yemi Osinbajo
Chief Rotimi Amaechi
Dr. Chris Ngige
Governor Yahaya Bello
Ibinabo Joy Dokubo
Ihechukwu Dallas-Chima
Senator Orji Uzor Kalu
Engr Dave Umahi
Rev Moses Ayom
Senator Rochas Okorocha
Gbenga Olawepo-Hashim
Ibrahim Bello Dauda
Dr. Tunde Bakare
Tein Jack-Rich
Asali: Legit.ng