Duk matashin da bai da N50m na sayan Fam, ba da gaske yake ba: Shugabar matan APC

Duk matashin da bai da N50m na sayan Fam, ba da gaske yake ba: Shugabar matan APC

  • Shugabar Matan jam'iyyar APC, Betta Edu, ta ce Duk wanda da bai da N50m na sayan Fam, ba da gaske yake ba
  • APC ta ce naira milyan dari kowani dan takara kujerar Shugaban kasa zai biya don yankan Fom
  • Amma duk matashin dake kasa da shekaru 40, an yi masa rahusa ya biya rabin kudin

Abuja - Shugabar matan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Betta Edu, ta ce duk matashin da ke son zama shugaban kasa a 2023 ya kamata ya iya mallakan N50 million.

Jam'iyyar APC a ranar Laraba ta sanar da farashin sayar da Fam din takarar kujerar shugaban kasa karkashin lemarta.

APC ta ce naira milyan dari kowani dan takarar kujerar Shugaban kasa zai biya don yankan Fom.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa na fitar da N100m don sayawa Tinubu fom din takara, Attajirin Dan kasuwa

Na gwamna kuwa, za'a sayar da Fam din N50m yayinda masu neman kujerar Sanata zasu kashe N20m.

APC har ila yau ta ce N10 za ta sayar da Fam ga masu neman kujerar yan majalisar wakilai sannan masu neman takarar kujerar majalisar jiha N2m.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma duk matashin dake kasa da shekaru 40, an yi masa rahusa ya biya rabin kudin.

Shugabar matan APC
Duk matashin da bai da N50m na sayan Fam, ba da gaske yake ba: Shugabar matan APC
Asali: Facebook

A hirarta da tashar Arise TV, Beta Edu tace akwai hanyoyin da matashi ya kamata ya bi don tara wannan kudi.

Tace:

"Idan kana son kula da yan Najeriya, ya kamata ace ka fi karfin milyan hamsin."
"Akwai hanyoyi da dama da matasa zasu iya tara kudi. Bai zama dole kudinka ba. Akwai hanyoyin samun kudin yakin neman zabe. Ku tuna, an rage musu kudin."
"Idan ba kada hanyar samun milyan hamsin kuma kana son zama shugaban kasa, toh akwai matsala. Ta yaya zaka iya rike amana idan aka baka kudin da suka fi haka yawa."

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan Boko Haram sun kai hari mashaya a Yobe, sun kashe 9, sun kona Kwalejin Fasaha

APC ta sanar da farashin da zata sayar da fam ga duk wadanda ke son takarar

APC ta ce naira milyan dari kowani dan takaran shugaban kasa zai biya don yankan Fom.

Na gwamna kuwa, za'a sayar da Fam din N50m yayinda masu neman kujerar Sanata zasu kashe N20m.

N10m za ta sayar da Fam ga masu neman kujerar yan majalisar wakilai sannan masu neman takarar kujerar majalisar jiha N2m.

Za'a fara sayar da Fam din daga ranar 22 ga Afrilu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel