Amfanin agwaluma 5 a jikin dan Adam

Amfanin agwaluma 5 a jikin dan Adam

Tabbass lafiya ita ce uwarjiki kuma kowa ya kwana lafiya shine ya so hakan. Akwai wasu tarin yayan itatuwa da ke da tarin alfanu sannan kuma basu da wata illa ga jikin dan Adam. sai dai mutane da dama basu san don haka ba hakan ne yasa muka lalubo maku wasu daga cikin amfanin agwaluma.

Wani sabon binciken kimiyya ya nuna cewa za a iya amfani da ganyayyaki da itacen Agwaluma wajen magance wasu cututtuka a jikin dan adam.

Amfanin agwaluma 5 a jikin dan Adam
Amfanin agwaluma 5 a jikin dan Adam
Asali: UGC

1. Agwaluma na maganin zazzabin Malaria mai naci ko wanda bai jin magani. Binciken wanda aka wallafa a kundin BMC Complementary and Alternative Medicine ya bayyana cewa wannan magani ka iya zama sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin duba da rashin nasarar da ake samu da sauran nau’ikan magunguna.

2. Agwaluma dai na dauke da sinadarin Vitamin C, wanda ke da matukar amfani a jikin dan adam.

3. Agwaluma na da matukar amfani ga mai dauke da juna biyu. Shan agwaluma na tsayar da amai da jiri wanda juna biyu ke haifarwa.

KU KARANTA KUMA: Mutane da dama sun mutu yayinda Boko Haram suka kai hari Rann

4. Sannan idan mutum baya so yayi kiba day a wuce misali sannan yana bukatar sinadarin gyaran idanu da zuciya toh agwaluma na taimakawa sosai wajen cimma hakan.

5. Yana kuma taimakawa wajen samun bacci cikin kwanciyar hankali. Sannan kuma yana rage ciwon gabbobin jiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng