Dakarun hadin gwiwa sun yi gagarumin nasara: Sun kashe kwamandojin ISWAP 10 da mayaka 100 a tafkin Chadi

Dakarun hadin gwiwa sun yi gagarumin nasara: Sun kashe kwamandojin ISWAP 10 da mayaka 100 a tafkin Chadi

  • Dakarun rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa sun yi nasarar kashe wasu kwamandoji da mayakan ISWAP
  • An kashe 'yan ta'addar ne a wani samame da sojojin Najeriya da Nijar da Kamaru suka kai a yankin tafkin Chadi
  • Mai magana da yawun MNJTF ya ce an kwato kayan abinci da makamai a yayin samamen da aka kai matsugunan yan ta'addan

Dakarun hadin gwiwa da ke yaki da Boko Haram (MNJTF) sun kashe yan ta’addan ISWAP da yawansu ya kai 100 ciki harda manyan kwamandojinsu 10 a yankin tafkin Chadi.

Babban jami’in yada labarai na rundunar soji na MNJTF, Kanal Muhammad Dole, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, ya ce sojojin sun yi nasarar afkawa mafakar yan ta’addan a wani farmaki da suka kai ta kasa da sama.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Sojoji sun yi gagarumin nasara: Sun kashe kwamandojin ISWAP 10 da mayaka 100 a tafkin Chadi
Sojoji sun yi gagarumin nasara: Sun kashe kwamandojin ISWAP 10 da mayaka 100 a tafkin Chadi Hoto: Nigerian Army
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa Dole ya ce an gudanar da harin ne karkashin rundunar Operation Lake Sanity da hadin gwiwar dakarun MNJTF daga Najeriya, Nijar da Kamaru da dakarun Operation Hadin Kai (OPHK- Nigeria).

Dole ya ce sojojin sun kai samame matsugunan ‘yan ta’addan a Zanari, Arina Woje, wadanda suka kasance manyan wuraren horonsu, da kuma wasu wurare da dama da ke kewayen yankin daga bangarori daban-daban a cikin mako guda da ya gabata.

A cewarsa, an kashe yan ta’addan ne bayan samun hare-haren sirri da rundunar hadin gwiwa ta kai ta sama a yankin tafkin Chadi.

Ya ce:

“Wasu daga cikin kwamandojin da aka kashe sun hada da Abubakar Dan Buduma, Abubakar Shuwa, Abu Ali, Abu Jubrilla da sauransu.
“Bugu da kari, an lalata muggan makamai iri daban-daban, jiragen ruwa da yawa, babura, kekuna da bama-bamai iri-iri.

Kara karanta wannan

Luguden jiragen Sojojin sama ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram fiye da 70

“A yayin samamen, an ceto mutane da dama wanda yawancinsu mata da yara ne da ke tsare a hannun yan ta’adda.
"An kwato kayan abinci da yawa, man fetur, haramtattun kwayoyi, kakin 'yan ta'adda da sauran kayayyakin amfanin gida kuma an lalata su nan take.”

Ya kara da cewa sojojin sun ci karo da irin wadannan hare-hare guda hudu, inda ya ce sojoji 18 sun samu raunuka a wadannan hare-haren, rahoton The Cable.

Dole ya kara da cewa an kwashe wadanda suka jikkata zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na sojoji daban-daban domin yi musu magani, yayin da sojoji uku da daya daga cikin jami’an CJTF suka rasa ransu.

Batun rashin tsaro: Tsohon ministan Buhari ya yiwa shugaban kasar wankin babban bargo

A wani labarin, tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gazawa yan Najeriya sannan cewa ya baiwa mutane da dama kunya ciki harda shi saboda ya kasa magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Manyan jaruman kannywood maza 4 da suka shafe sama da shekaru 20 suna fim kuma ake yi da su har yau

Dalung ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 10 ga watan Maris.

Tsohon ministan ya kuma koka kan cewa shugaban kasar na raba iko tare da kasurgumin shugaban yan bindiga na arewa maso yamma, Bello Turji da kuma mayakan ISWAP sakamakon gazawarsa wajen magance rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng