Ba za'a daina kashe mutane ba muddin ba'a bari jama'a su mallaki nasu bindigogin ba, Dan majalisa

Ba za'a daina kashe mutane ba muddin ba'a bari jama'a su mallaki nasu bindigogin ba, Dan majalisa

  • Dan majalisa, Yusuf Gagdi, yace yan bindiga ba zasu daina yiwa mutane kisan kiyashi ba a kasar nan sai an halasta rike makamai ga kowa
  • Wannan ya biyo bayan kisan al'ummar mazabarsa sama da mutum 100 a farkon makon nan
  • A baya, gwamnonin Taraba da Katsina sun yi kira irin na wannan dan majalisa na halasta rike bindiga

Plateau - Dan majalisar wakilai, Yusuf Gagdi, ya yi kira majalisar dokoki ta kafa dokokin halastawa yan Najeriya mallakar nasu bindigogi domin kare kawunansu.

Yusuf Gagdi wanda ke wakiltar mazabar Pankshin, Kanke da Kanam ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a Kanam.

Dan majalisan ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci wasu garuruwa a Kanam da Wase da yan bindiga suka kaiwa hari, rahoton Vanguard.

Mun kawo muku rahoton cewa yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata sun hallaka mutum 106 a Kanam da Wase kuma suna kona gidaje.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta fara rabon ton 40,000 na hatsi don Easter da Azumi ga talakawa

Gagdi, Dan majalisa
Ba za'a daina kashe mutane ba muddin ba'a bari jama'a su mallaki nasu bindigogin ba, Dan majalisa Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

A cewar Yusuf Gagdi, halasta rike makami na da muhimmanci wajen maganace wannan hare-hare da kashe-kashe.

Yace:

"Idan muna son dakile hare-haren nan, toh mu kafa dokokin halastwa mutane daukar makamai."
"Misali, idan masu kai hari suka da yan gari na da makamai, ba zasu je ba, kuma idan suka je, adadin wadanda za'a kashe ba zai kai haka ba."
"Amma dole ne a kafa dokokin rike makaman, duk wanda yayi amfani da shi ta hanyar da bai dace ba a daureshi, ko a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng