Hotuna: Zulum ya gwangwaje 'yan gudun hijirar Monguno da N275m, kayan abinci, sutura
- Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya raba wa 'yan gudun hijira N275m, kayan abinci da zannuwa a garin Monguno na jihar
- Zulum ya samu rakiyar bulaliyar majalisa, Barista Mohammed Tahir Monguno tun ranar Alhamis inda suka kwana a Mafa
- Sun karasa Monguno inda aka raba wa mata zannuwa, sikari, N5,000 da kuma maza suka samu buhunan shinkafa bibbiyu da masara
Monguno, Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya garzaya garin Monguno tun ranar Alhamis inda ya duba yadda ake raba miliyan dubu dari biyu da saba'in da biyar tare da buhunan abinci da kuma sutturu da aka raba wa gidaje 90,000 na 'yan gudun hijira.
Wannan irin tallafin, wanda Zulum ya saba kai wa tun shekaru uku da suka gabata, yana daga cikin kokarinsa na karfafa guiwar yankunan da hare-haren Boko Haram suka shafa, taimaka musu da yanayin rayuwa yayin da suke komawa noma da sauran kasuwanci domin tallafawa rayuwarsu.
Tallafin kudin ana ganin amfaninsa domin kuwa yana hana jama'a zama masu leken asiri ga 'yan Boko Haram sakamakon tsananin talauci, da kuma kwadayin yadda suke bai wa jama'ar N5,000 a matsayin kyautatawa.
Zulum tare da bulaliyar majalisar wakilai, Barista Mohammed Tahir Monguno, sun hau mota daga Maiduguri a ranar Alhamis inda suka kwana a Mafa tare da isa Monguno a ranar Juma'a da safe domin fara rabon.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Monguno ta kasance masaukin 'yan gudun hijira daga kananan hukumomi biyar na yankunan tafkin Chadi, tare da 'yan gudun hijira da suka dawo daga jamhuriyar Nijar bayan sun tserewa farmakin Boko Haram tsakanin 2013 zuwa 2014.
Bayan tatatunawa da 'yan gudun hijiran da kuma wadanda suka dawo Monguno, Gwamna Zulum a ranar Juma'a ya duba yadda ake raba zannuwa, sikari da N5,000 ga mata 55,000.
Bayan kammalawa da bangaren mata a ranar, Zulum ya fara da bangaren maza a tsakar daren Asabar inda magidanta 35,000 suka samu tallafi. Kowanne ya samu buhun shinkafa bibbiyu da masara.
Hotunan Zulum a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi, ya bai wa masu komawa gida N.5b
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gwangwaje ‘yan gudun hijira fiye da mutane 5000 da rabin biliyan daya, Daily Trust ta ruwaito.
‘Yan gudun hijiran sun nuna bukatar komawa gidajensu ne don su cigaba da rayuwa. Gwamnan ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran da misalin 5:45am inda aka fi sani da Bakassi a Maiduguri.
A takardar wacce hadimin gwamna Zulum ya saki, ya ce gwamnan ya yi sa’o’i 7 ya na jagorantar raba kudade da kayan abinci yayin da ya kai ziyarar ta ba-zata don tallafa wa mabukata da marasa gida saboda wasu mutanen su na zuwa sansanin ‘yan gudun hijiran tun safe sai dare su ke komawa gidajensu da sunan su ‘yan gudun hijira ne.
Asali: Legit.ng