'Yar Kano Ta Zama Gwarzuwar Shekara A Taron Karrama Masu Sana'ar Hannu, Ta Samu Lambar Yabo 3
- Fatima Sakibu, wata bakanuwa yar shekaru 14 mai sana'ar saka tile ta lashe lambobin yabo uku a taron da aka yi a Abuja
- Fatima, wacce ke babban ajin sakandare a farko ta mika godiyarta da iyayenta musamman mahaifinta wanda ya koya mata sana'ar
- Yayin nuna farin cikinta bisa lambobin yabon da ta lashe, ta bayyana cewa tana fatan zama Injiniya idan ta kammala karatunta
Wata yarinya mai shekaru 14 yar Kano, Fatima Sakibu, ta lashe lambobin yabo uku a taron karrama masu sana'ar hannu na gine-gine da bajekolin basira da aka yi a dakin taro na Moshood Abiola Stadium a Abuja.
Matashiyar mai aikin saka tile ta lashe lambobin yabo uku a wurin taron; itace ta zama na daya a bangaren sana'ar saka tile, ita ce ta gwarzuwa a bangaren mata masu sana'ar hannu kuma ita ce gwarzuwan matashiyar mai sana'ar hannu.
Ta samu lambobin yabon ne bayan Daily Trust ta wallafa rahotanni a game da yadda matashiyar Fatima ke nuna bajinta a sana'ar da maza ne suka fi yawa.
Fatima ta koyi sana'ar saka tile ne daga wurin mahaifinta shekaru kadan da suka shude kuma hakan bai hana ta cigaba da zuwa makaranta ba.
Fatima ta bayyana farin cikinta bisa lambobin yabon da ta samu
Ta bayyana matukar farin cikinta bisa lashe lambobin yabon, yayin da ta ke mika godiyarta ga iyayenta bisa gudunmawar da suka bada a rayuwarta musamman mahaifinta wanda ya koya mata sana'ar saka tile.
Matashiyar mai sana'ar saka tile, wacce yanzu ta ke aji na farko a babban sakandare, ta ce za ta cigaba da yin sana'ar, kuma tana fatan zama Injiniya idan ta kammala karatu, rahoton Daily Trust.
Kungiyar Kula Da Lafiyan Masu Sana'o'i, (Occupational Safety and Health Association) ce ta ke shirya taron bada lambar yabon a duk shekara domin karrama mutane masu basira daban-daban.
Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota
A baya, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki motarsa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.
Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.
Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.
Asali: Legit.ng