Matashin dan kasuwa gwal ya kashe babban abokinsa a Neja, ya tafi da motarsa da kudi N3.5m

Matashin dan kasuwa gwal ya kashe babban abokinsa a Neja, ya tafi da motarsa da kudi N3.5m

  • Ana neman wani matashi ruwa a jallo bisa zargin kisan abokin kasuwancinsa a Minna, jihar Neja
  • Kakakin hukumar yan sanda yace an tsinci gawar Hassan a gidan babban abokinsa ne bayan zuwa wata harkar ciniki
  • Jama'an unguwar sun ce sun ga Bashir cikin motar Hassan ya arce da wasu makudan kudade

Neja - An tsinci gawar wani matashin dan kasuwar, Hassan Shehu, a gidan wani babban abokinsa a Tudun Fulani, karamar hukumar Bossi ta jihar Neja, Arewa maso tsakiyar Najeriya.

TheNation ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, 2022.

Jami'an yan sanda yanzu na neman abokin mai suna Bashir bayan an tsinci gawar Hassana gidansa.

Majiyoyi sun bayyana cewa Bashir ya kira Hassan a waya ne, yana mai fada masa cewa yana da zinarin N5million na sayarwa.

Kara karanta wannan

Bidiyon cikin tamfatsetsen gidan Hassan Ayariga mai dakunan bacci 10, silma da wurin aski

Tun da abokai ne kuma harka daya suke yi. Sai Hassan ya fadawa Bashir N3.5million yake da shi kuma Bashir yace ba matsala ya kawo.

Majiyar tace Hassan ya tafi gidan Bashir da kudi cikin motarsa kirar Peugeot 206 mai lambar Legas EPE141 EG.

Yan gidan su Hassan shuke yi wannan shine lokacin karshe da suka ga Hassan, sai kuma lokacin da aka ce an ga gawarsa a gidan Bashir.

Matashin dan kasuwa
Matashin dan kasuwa gwal ya kashe babban abokinsa a Neja, ya tafi da motarsa da kudi N3.5m Hoto: TheNation
Asali: Facebook

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da labarin yace makwabta su ga Bashir yana guduwa cikin motar Hassan.

Bincike ya nuna cewa Bashir ya cakawa Hassan kaifi a wuya, inda hakan yayi sanadiyar mutuwarsa.

A cewarsa:

"A ranar 12/04/2022, misalin karfe 1700hrs, an samu kirar waya cewa an ga gawar namiji a cikin wani daki a Tudun Fulani a Bosso, Minna.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da yan Boko Haram sun fara alaka da juna, Gwamnatin tarayya ta sanar

"Binciken farko ya nuna cewa an cakawa marigayin kaifi a wuya, kuma wani Bashir ya gayyacewsa, don sayar masa da wasu gwala-gwalai."
"Bashir, da ake zargin shi ya kashe marigayin, an ce an gansa cikin motar marigayin da kudi yana guduwa."

Abiodin yace har yanzu ana kokarin ganin an damke Bashir.

Saurayi, Ahmed, Ya Jagoranci Garkuwa Da Budurwarsa, Ya Karɓi Fansar N2m Daga Hannun Iyayenta

A Abuja kuwa, Rundunar ‘yan sandan ta kama wani Ahmed bisa zarginsa da garkuwa da budurwarsa, Hannatu Kabri bayan hada kai da wani Uchenna Daniels.

Daniels ya sace Kabri a Abuja a ranar 31 ga watan Maris sannan ya zarce da ita Legas.

News Wire NGR ta rahoto yadda ‘yan sanda suka dage wurin farautar masu laifin wanda har ya kai ga an kama Daniels.

Asali: Legit.ng

Online view pixel