Nayi matukar farin cikin yafewa Dariye da Nyame, Buhari ya amsa kira na: Jonah Jang

Nayi matukar farin cikin yafewa Dariye da Nyame, Buhari ya amsa kira na: Jonah Jang

  • Sanata Jonah Jang ya bayyana farin cikinsa bisa amsa kiransu da Shugaba Buhari ya yi a makon nan
  • Jang ya ce al'ummar Jos da Taraba na matukar farin cikin bisa hallacin da Shugaba Buhari ya yi
  • Majalisar koli ta kasa karkashin jagorancin Shugaban kasa ta yafewa tsaffin gwamnoni biyu da suka zalunci al'umma suka sace biliyoyi

Jos - Tsohon Gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang, ya bayyana cewa afuwar da shugaba Buhari ya yiwa tsohon gwamnan Plateau Joshua Dariye da tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame abin farin ciki ne.

Sanata Jang wanda ya bayyana farin cikinsa bisa wannan abu ya yi kira da tsaffin gwamnonin biyu idan sun fito su mayar da hankali wajen cigaban kasa.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Clinton Garuba, ya fitar ranar Juma'a, ya mika godiyarsa ga Shugaba Muhammadu Buhari, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sakin Dariye da Nyame: Bayan kwashe shekaru 11 a kotu, da kashe miliyoyin kudi, Shikenan: Lauyoyin EFCC

Yace:

"Labarin cewa majalisar kolin tarayya ta yafewa tsohon gwamnan Plateau, Cif Joshua Chibi Dariye da tsohon Gwamna Jolly Nyame na Taraba abin farin ciki ne ga al'ummar Plateau da Taraba musamman lokacin da ake cikin matsaloli a kasar nan."
"Muna godewa shugaban kasa bisa amsa kiran mutane da yawa ciki har da Sanata Jonah Jang wanda a 2021 ya yi kira ga shugaban kasa ya yafewa Sanata Dariye da Gwamna Jolly Nyame, domin basu damar taimakawa cigabar kasar."

Nayi matukar farin cikin yafewa Dariye da Nyame, Buhari ya amsa kira na: Jonah Jang
Nayi matukar farin cikin yafewa Dariye da Nyame, Buhari ya amsa kira na: Jonah Jang
Asali: Facebook

Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

A jiya, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, a ranar Juma’a, ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisar kolin kasa bisa afuwar da suka yi wa tsaffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba, Sanata Joshua Dariye da Rabaran Jolly Nyame.

Kara karanta wannan

Nayi matukar kaduwa bisa ambaliyar ruwan sama a kasar Afrika ta Kudu, Shugaba Buhari

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ortom, Nathaniel Ikyur ya fitar, ya ce gwamnan ya godewa shugaba Buhari da majalisa da kuma gwamnatin tarayya bisa wannan matakin duk da cewa ya yarda cewa lallai an koyi darassu masu amfani daga lamarin.

Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga abokai da iyalai da abokan siyasa na shugabannin biyu da suka ba su goyon baya a tsawon lokacin da suke gidan yari, kamar yadda AIT ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng