Gwamnatin Tarayya ta fara rabon buhunan abinci kamar yadda Buhari ya bada umarni
- A makon nan gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin raba kayan abinci ga wadanda ke bukata
- Kwanaki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi a rabawa al’umma hatsi a wannan lokaci
- Hakan zai sa masu azumi da bikin easter su samu abinci, kuma a rage radadin tsadar hatsi a kasuwa
Abuja - A ranar Alhamis, 14 ga watan Afrilu 2022, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin raba hatsi domin a rage radadin tsadar kayan abinci a kasar nan.
Punch ta ce Ministan harkar noma da raya karkara, Mohammad Abubakar ya kaddamar da wannan shiri a sansanin gudun hijira a Karamiji a garin Abuja.
Mohammad Abubakar ya ce an zabi wannan wuri ne domin wadanda suke gudun hijira su na cikin wadanda suka fi kowa bukatar kayan abinci a wannan lokaci.
Baya ga hatsi, Ministan ya bayyana cewa sauran kayan da ake rabawa sun hada da ganye da abincin gidan gona da za su jawo farashi ya yi sauki a kasuwa.
“Bari in ce, tsadar kaya a kasuwanni ya taba farashin kayan abinci dabam-dabam, daga ciki har da kaji da sauransu.”
“Rabon zai kunshi kayan lambu saboda su na cikin wadanda ake bukata. A dalilin haka, za mu rabawa al’umma.”
Za a hada da sauran ma'aikatu
“Ba ma’aikatar noma da raya karkara kurum za ta yi aikinba, har da ma’aikatar jin kai da bada agajin gaggawa.”
-Mohammad Abubakar
An rahoto Ministan ya na cewa takawararsu watau ma’aikatar jin kai da bada agajin gaggawa za ta raba metric tan 12, 000 na wadannan kayan abinci ga mabukata.
Ministan ya shaidawa ‘yan jarida cewa za su hada-kai da ma’aikatar matasa da wasanni da kuma sauran hukumomi domin ganin an raba hatsin ga mafi bukata.
Rumbuna a ciki su ke
Abubakar ya ce Najeriya ta na da metric ton sama da 90, 000 na hatsi saboda irin wannan rana, kuma yanzu ana cika rumbunan yayin da ake rabon wasu kayan.
Ministan ya ce ana ta sayen kayan abinci ana ajiyewa a dakin ajiyar saboda jiran rana irin ta yau.
Zan bunkasa tattali - Kalu
An rahoto Sanata Orji Uzor Kalu yana cewa a cikin shekaru hudu kacal zai iya rikidar da tattalin arzikin kasar nan har ta kai ya zama kamar na Amrka ko Jafan.
Orji Uzor Kalu ya yi alkawarin cewa karfin tattalin Najeriya zai zama kamar na manyan kasashe idan ya yi nasarar lashe zaben takarar Shugaban kasa a 2003.
Asali: Legit.ng