Da Dumi-Dumi: Majalisar Shugabannin Ƙasa sun sanya ranar ƙidaya yawan Yan Najeriya

Da Dumi-Dumi: Majalisar Shugabannin Ƙasa sun sanya ranar ƙidaya yawan Yan Najeriya

  • Majalisar shugabannin ƙasar nan tsofaffi da na kan madafun iko sun amince da gudanar da ƙidaya a watan Afrilu, 2023
  • Shugaban hukumar ƙidaya ta ƙasa, NPC, Nasir Isa-Kwarra, ya ce hukumarsu zata yi amfani da fasahohin zamani da dama
  • Ministan Shari'a, Abubakar Malami, da ministan ayyuka na musamman sun bayyana abubuwan da aka amince musu a taron

Abuja - Majalisar magabatan ƙasar nan ta amince da gudanar da ƙidaya ta ƙasa a watan Afrilu, 2023 bayan kammala babban zaɓe, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Darakta Janar na hukumar kidaya ta ƙasa NPC, Nasir Isa-Kwarra, shi ya bayyana haka ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar bisa jagorancin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Isa-Kwarra ya ƙara da cewa hukumar NPC zata gudanar da gwajin kidaya a watan Yuni, 2022 bayan jam'iyyun siyasa sun kammala harkokin su na zaɓen fidda gwani.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaron Najeriya kan halin da ake ciki

Taron Majalisar Magabata ta ƙasa a Aso Villa.
Da Dumi-Dumi: Majalisar Shugabannin Ƙasa sun sanya ranar ƙidaya yawan Yan Najeriya Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Shugaban NPC wanda ya tuna ƙidaya ta karshe da aka gudanar a 2006, ya ce hukumarsa zata yi amfani da Fasahar zamani daban-daban yayin aikin ƙidaya.

Punch ta rahoto Isa-Kwarra ya ce:

"Abu ne mai matuƙar muhimmanci saboda wasu tsokacin da na yi game da muhimmancinsa ga ƙasa. Ta hanyar ƙidaya muke tara bayanan da muke amfani da su wajen tsare-tsaren kawo cigaba a matakai uku na gwamnati da bagaren masu zaman kansu."
"Duk suna bukatar kidaya, idan kana ɓangaren masu zaman kan su, kana samar da wasu abubuwa, ba kokwanto kana bukatar yawan mutanen wannan yankin don kasan yadda zaka tafiyar da kasuwancin ka."
"Saboda haka bayanan da ake tattara wa a ƙidaya suna da matuƙar muhimmanci. A yanzu waɗan da muke da su a hannu kiyasi ne kawai, muna bukatar ainihin bayanai da alƙaluma na haƙiƙa."

Kara karanta wannan

Ta fallasu: Abinda Shugaba Buhari ya faɗa wa Gwamnan da ya sanar masa zai nemi shugaban ƙasa a 2023

Sauran abubuwan da aka amince da su a taron

Antoni Janar na ƙasa kuma ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya ce majalisar ta amince da buƙatu 159 cikin 162 da ya gabatar waɗan da suka shafi yafiya ga Fursunoni a gidajen gyaran halin ƙasar nan.

Ministan ayyuka na musamman, George Akume, ya ce majalisar ta amince da ba da lambobin yabo ga yan Najeriya 434 waɗan da suka yi zarra a fannoni daban-daban.

A wani labarin na daban kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP ya ɗauki alƙawarin gyara Najeriya a shekararsa ta farko bayan zama shugaban ƙasa a 2023

Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP ya lashi takobin kawo sauyi a Najeriya cikin shekara ɗaya da zaran yan Najeriya sun ba shi dama.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, ya ce idan bai gyara Najeriya a wannan lokacin ba a masa kiranye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262