Wata uku da shiga 2022, majalisa ta amince da kasafin kudin 2022, za a ci bashin N965.42bn
- Tun da farko dai majalisar dattawa ta samu bukata daga Buhari na amincewa da gyara tsarin kasafin kudin 2022
- A ranar Alhamis, 14 ga Afrilu, Majalisar Dokoki ta Kasa ta zartar da gyare-gyare ga Dokar Kasafin Kudi na 2022 da Tsarin Kudi na 2022
- A halin da ake ciki, gibin kasafin kudin ya karu da Naira biliyan 965.42 zuwa Naira tiriliyan 7.35, wanda za a yi shi ta hanyar karbo sabon rance daga kasuwannin cikin gida
Majalisar dokokin Najeriya ta amince da gyare-gyare kan dokar kasafin kudi na 2022, wanda ya kawo gibi a kasafin kudin gwamnatin tarayya da Naira biliyan 965.42 zuwa Naira tiriliyan 7.35.
Majalisar dattawa da ta wakilai, sun yi nazari tare da amincewa da rahotanni kan kudurorin gyaran fuska ga kasafin ne a yau Alhamis, bisa bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar tun farko.
Yayin da ake ta cece-kuce kan man fetur, majalisa ta amince da bukatar Buhari na kashe N4tr a tallafin mai
Majalisar dokokin tarayya ta amince da sabon farashin mai na dalar Amurka 73 kan kowacce ganga, sabon adadin man da za a ke hakowa zuwa miliyan 1.600 a kowace rana, da kuma kudin tallafin man fetur na Naira tiriliyan 4, inji rahoton The Punch.
An rage kudaden ayyukan da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa zuwa sama da Naira biliyan 200 daga N352.80bn, yayin da hasashen kudaden shiga mai zaman kansa na Gwamnatin Tarayya ya ya koma N400bn.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sabon ci gaban da aka samu
Haka kuma an amince da karin wani tanadi na Naira biliyan 182.45 don biyan bukatun rundunar ‘yan sandan Najeriya da kuma samar da Naira biliyan 76.13 na biyan basussuka a cikin gida, tare da rage rarar kudaden doka da N66.07bn.
Rage-ragen da aka samu na kashe kudade
Sauyen-sauyen da aka samu a dokar sun kasance kamar haka:
- NDDC da gibin N13.46bn, daga N102.78bn zuwa N89.32bn
- NEDC da gibin N6.30bn, daga N48.08bn zuwa N41.78bn
- UBEC da gibin N23.16bn, daga N112.29bn zuwa N89.13bn
- Asusun Kula da Lafiya da gibin N11.58bn, daga N56.14bn zuwa N44.56bn
- NASENI kuma da gibin N11.58bn, daga N56.14bn zuwa N44.56bn
Yayin da ake ta cece-kuce kan man fetur, majalisa ta amince da bukatar Buhari na kashe N4tr a tallafin mai
A wani labarin, majalisun dokokin kasar nan sun amince da bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bijiro da ita na ware naira tiriliyan 4 na kudin tallafin man fetur, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
Majalisar dattawa da ta 'yan majalisu sun amince da bukatar shugaban kasar ne bayan sun yi la’akari da rahotannin kwamitocinsu kan harkokin kudi.
Amincewar ta biyo bayan bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na sake fasalin kasafin kudin shekarar 2021.
Asali: Legit.ng