Jihohin Arewa su ne a gaba yayin da aka kashe mutane 2, 968 a cikin watanni 3 a 2022
- Tsakanin Junairu zuwa watan Maris na shekarar bana, an kashe Bayin Allah kusan 3000 a Najeriya
- Alkaluman da Nigeria Security Tracker ta fitar ya nuna cewa an kuma yi garkuwa da mutum 1400
- Jihohin da suka fi fuskantar wannan matsala sun hada da Neja, Kaduna, Zamfara duk a yankin Arewa
Nigeria - Akalla mutane 2, 968 aka kashe daga watan Junairu zuwa Maris a shekarar nan ta 2022. Haka zalika an yi garkuwa da mutane 1, 484 a kasar nan.
Kamar yadda Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Laraba, alkaluman da Nigeria Security Tracker (NST) suka fitar a makon nan ya tabbatar da haka.
Nigeria Security Tracker su kan tattara bayanai a game da rayukan da aka rasa a Duniya. Sannan su na tara alkaluma a kan garkuwa da mutane da ake yi.
NST ta tabbatar da cewa ana fama da miyagun ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan Boko Haram a Arewa. A Kudu, Sojojin ESN na IPOB ne suka fitina jama’a.
Tsagerun Neja-Delta su kan yi ta’adi a jihohi irinsu Ribas, Kuros Riba da Akwa Ibom har gobe. A kudu maso yamma ana kukan ‘yan fashi da kungiyoyin asiri.
Adadin rayukan da aka rasa
Alkaluman sun bayyana cewa a yankin Arewa maso yamma ne aka fi fama da kashe-kashe. A cikin watanni ukun farko na bana, an kashe mutum har 1, 103.
Yankin Arewa maso tsakiya ne ya zo na biyu a wannan lokaci da mutuwar mutum 984. Sannan a shiyyar Arewa maso gabas an yi rashin akalla mutum 488.
Daga Junairu zuwa Maris, an rasa rayuka 181 a Kudu maso gabas. A wannan sa’ili ne aka kashe mutane 127 da 85 a Kudu maso yamma da kudu maso kudu.
Mutane 2000 sun mutu a jihohi 5
A takaice dai an hallaka mutane 2, 575 (fiye da 85%) daga bangaren Arewacin Najeriya. A gefe guda kuma, a yankin Kudu an kashe mutane 393 (kusan 15%).
Jihohin da lamarin rashin tsaro ya fi kamari su ne Neja (840), Zamfara (404), Borno (392), Kaduna (332), sai Kebbi (114). A jihohin biyar, an rasa rayuka 2, 082.
Garkuwa da mutane a 2022
A watannin nan uku kuma an yi garkuwa da mutane 1, 354 a yankin Arewa (91%). Jaridar ta ce ana da labarin satar mutane 130 a Kudancin Najeriya (9%).
Mutum 623 aka dauke a watan Junairu, a watan Fubrairu aka sace 342, sai aka samu 519 a Maris. Abin ya fi yawa ne a Neja, Kaduna, Zamfara, Katsina da Kogi.
Tsageru su na jawowa kasa asara
Kwanaki aka ji labari shugaban kamfanin mai na kasa na NNPC, Mele Kolo Kyari ya koka a game da yadda masu fasa bututun mai ke cin karensu babu babbaka.
Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe
Bayan haka ana fama da matatun da ke satar danyen mai a Kudu. Wannan matsala ta jawo ana maganar gwamnatin tarayya ta yi asarar $1.5bn a shekarar nan.
Asali: Legit.ng