Da Duminsa: Kotun Koli ta tabbatar da ɗaurin wata shida kan tsohon shugaban Fansho, Yakubu

Da Duminsa: Kotun Koli ta tabbatar da ɗaurin wata shida kan tsohon shugaban Fansho, Yakubu

  • Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke wa tsohon daraktan Fansho na ƙasa, John Yakubu
  • Hukuncin dai ya ƙunshi ɗaurin shekara 6 a gidan gyaran hali da kuma maida kudin da ya amince sun ɓata asusun gwamnati
  • A shekarar 2018 Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke masa wannan hukuncin, kuma tuni aka kai shi Kuje

Abuja - Kotun Koli ta Najeriya, ranar Laraba, ta tabbatar da hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara na ɗaure tsohon Daraktan Fansho na ƙasa, John Yakubu, tsawon shekara 6 a gidan Yari.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Kotun Allah ya isan ta kuma umarci Yakubu ya maida wa gwamnatin tarayya Naira Biliyan N22.9bn.

A shekarar 2018, Kotun ɗaukaka ƙara ta ɗaure Yakubu a gidan gyaran Hali bisa kama shi da laifin karkatar da kuɗin gwamnatin tarayya biliyan N22.9bn.

Kara karanta wannan

Idan ban gyara Najeriya a shekara ɗaya ba ku mun kiranye, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023

Shugaban daraktan Fansho, John Yakubu.
Da Duminsa: Kotun Koli ta tabbatar da ɗaurin wata shida kan tsohon shugaban Fansho, Yakubu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Waɗan nan kuɗin dai wani ɓangare ne na kuɗin Fanshon hukumar yan sanda wanda ya amince a gaban babbar Kotun tarayya dake zama a Abuja cewa ya wawure su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tabbatar da Hukuncin Kotu

Alƙalin Kotun mai Shari'a, Tijjani Abubakar, yayin da yake yanke hukuncin kan korafin ɗaukaka ƙara da wani Yusuf ya shigar, ya tabbatar da hukuncin ɗaukaka ƙara na 2018.

Alƙalin ya ce wannan ɗaukaka ƙarar da bukatar jingine hukuncin ɗaurin shekara 6 da aka yanke masa abun takaici ne.

Ya kuma ƙara da yanke cewa mutanen da suka cutu sanadin aika-aikan tsohon Daraktan sun cancanci a rama musu, kuma ta hanyar adalci ne kaɗai za'a tabbatar da haka.

Channels tv ta rahoto cewa Yusuf ya maka gwamnatin tarayya a gaban Kotun Koli ne yana mai bukatar ta jingine ɗaurin shekara 6 da Kotun ɗaukaka ƙara da yanke wa tsohon Darakta.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game shugaban cibiyar Kididdigan Najeriya da ya mutu yau

Haka nan tsohon darakatan, wanda ke zaman ɗaurin shekara 6 a gidan gyaran halin Kuje, ya roƙi Kotu ta jingine batun maida biliyan N22.6bn asusun gwamnati da Kotun baya ta umarce shi.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun harbe ɗan kasuwa har Lahira kwanaki kafin Ɗaura Aurensa

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun harbe wani babban ɗan kasuwa a jihar Ebonyi mako ɗaya kafin ɗaura aurensa.

Bayanai sun nuna cewa makasan sun halaka mutumin mai suna Chukwu a gaban matar da zai aura, suka kwace mata waya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262