Ramadaniyyat 1443: Tsakanin Ibada Da Al'ada, Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Ramadaniyyat 1443: Tsakanin Ibada Da Al'ada, Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

Tsakanin Ibada Da Al'ada

1. Duk wani tasaruffi na ɗan'adam a maganganunsa da ayyukansu bai wuce iri biyu ba:

Na ɗaya, Ibadu, waɗanda su ne addininsa.

Na biyu, al'adu, waɗanda su ne gudanar da mu'amalolin rayuwarsa ta yau da kullum.

2. Binciken ƙwaƙwaf a cikin ƙa'idoji na shari'ar Muslunci ya tabbatar da cewa, duk wata ibada ba za ta tabbata ba sai ta hanyar shari'a kaɗai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Amma al'adu na rayuwar mutane ta yau da kullum, shari'a ta nuna cewa, babu abin da ake haramta musu daga ciki sai abin da Allah shi da kansa ya haramta.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Adalcin Shaikhul Islam Ibn Taimiyya (RH), Sheikh Dr Sani Rijiyar Lemo

4. Domin umarni da hani su ne shari'ar Allah. Ibada kuwa dole ne ta zamanto abin da aka yi umarni da aikta shi. Duk abin da bai tabbata ba ta hanyar umarnin Allah da Manzonsa, to ta yaya zai zama shari'ar Allah?

5. Hakanan duk wata al'ada da shari'a ba ta yi hani a kanta ba, to ba za a yi mata hukunci da haramun ba.

Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo
Ramadaniyyat 1443: Tsakanin Ibada Da Al'ada, Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo Hoto: Mal Sani Umar Rijiyar/Lemo
Asali: Facebook

6. Saboda haka ne Imamu Ahmad da sauran malaman hadisi suke cewa: ƙa'ida dangane da ibada ita ce, sai an samu nassi daga Allah ko Manzonsa. Ba za a ɗauki wani abu a matsayin addini ba har sai da izinin Allah, idan kuwa ba haka ba, to za mu shiga ƙarƙashin faɗar Allah: (Ko dai suna da wasu abokan tarayya ne da suka shar’anta musu wani abu na addini wanda Allah bai yi izinin yin sa ba?..) [Shura, aya ta 21].

7. Hakanan kuma ƙa'ida game da al'adu ita ce, an yi afuwa da rangwame, ba za a haramta wata al'ada ba sai wadda Allah (SAW) da kansa ya haramta. Idan kuwa ba haka ba, to za mu shiga ƙarƙashin faɗar Allah: (Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin abin da Allah Ya saukar muku na arziki, sannan kuka mayar da wani haram wani kuma halal”..) [Yunus, aya ta 59].

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Abubuwan Da Suke Hana Yin ƙarya, Dr Sani Rijiyar Lemo

[Duba, Ibn Taimiyya, Majmu'ul Fatawa, juzu'i na 29, Shafi na 16-17].

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng