Yadda shugaban LCCI ya rushe da kuka kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan

Yadda shugaban LCCI ya rushe da kuka kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan

  • Asiwaju Michael Olawole-Cole, shugaban kungiyar 'yan kasuwa da masana'antu ta jihar Legas ya koka da tabarbarwar tattalin arzikin kasar nan
  • Olawole-Cole ya fashe da kuka yayin da yake jawabi ga manema labarai kan yadda kayayyaki ke tashi kuma za su cigaba da tashi saboda wasu dalilai
  • Shugaban LCCI ya nuna damuwarsa kan ababen da suka shafi daurewar basussuka, kasuwar musayar kudade, bunkasa manufofin hada-hadar kudi, cinikayyar kasashen waje da sauransu

Legas - Shugaban kungiyar 'yan kasuwa da masana'antu ta jihar Legas, LCCi, Asiwaju Michael Olawale-Cole, ya fashe da kuka yayin da yake tsaka da jawabi ga manema labarai kan halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Olawale-Cole, yayin jawabi a Legas a ranar Talata, ya bayyana damuwarsa kan yadda kayayyaki ke tashi a kasar wanda ya kai kashi 15.70 a watan Fabrairu, kashi 15.60 a watan Janairun 2022.

Kara karanta wannan

Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo

Yadda shugaban LCCI ya rushe da kuka kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan
Yadda shugaban LCCI ya rushe da kuka kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda yace, ana tsammanin kaya za su cigaba da tashi sakamakon yakin Rasha da Ukraine, samuwar abinci za ta girgiza, tsarikan cinikayya tsakanin kasashe za su sauya, farashin makamashi zai tashi, rashin tsaro zai karu a manyan jihohin da ake samar da abinci kuma hakan zai matsantawa farashi.

Within Nigeria ta ruwaito cewa, ya bayyana cewa, daidaita manyan tsare-tsare na tsarin kasafin kudi don magance matsalolin da aka gano za su taimaka matuka wajen daidaita matsalar hauhawar farashin kayayyaki a cikin gajeren lokaci.

Shugaban na LCCI ya kara da nuna damuwarsa kan batutuwan da suka shafi daurewar basussuka, kasuwar musayar kudade, bunkasa manufofin hada-hadar kudi, cinikayyar kasashen waje, shigo da manyan kayayyaki, yakin Rasha da Ukraine, satar mai, bangaren wutar lantarki, da sauransu.

Kara karanta wannan

Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamun daukaka ne, In ji dan majalisa daga arewa

Ya ce lamarin ya kai wani yanayi mai cike da fargaba, musamman ma da farmaakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ya yi sanadin mutuwar jama'a masu yawa.

Buhari: Da gaske muke wajen ganin an ceto mutum miliyan 100 daga talauci a kasa

A wani labari na daban, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba da wasa gwamnatinsa ta ke yi a maganar maganin talauci ba.

Mai girma Muhammadu Buhari wanda ya ce babu gwamnatin da ta kawo tsare-tsare da za su taimaka wa matasa, ya inganta kokarin gwamnatinsa.

Shugaban kasar yayi magana ta dandalin sada zumunta na zamani na Twitter, yace an kara yawan mutanen da suke amfana da tsare-tsaren gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel