Osinbajo ya fita da APC ta Legas, ya koma ta jihar Ogun: Mai magana da yawunsa

Osinbajo ya fita da APC ta Legas, ya koma ta jihar Ogun: Mai magana da yawunsa

  • Mataimakin shugaban kasa tuni ya canza takardar zama dan APCn sa daga Legas zuwa jihar Ogun
  • Osinbajo dai dan asalin jihar Ogun amma rayuwarsa ta zama da siyasa a jihar Legas take
  • Masu sukarsa sun bayyana cewa a zaben 2019, ko rumfar zabensa dake VGC Legas bai iya kawowa ba

Abuja - Laolu Akande, mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa mai gidansa ya fita daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC na jihar Legas.

Wannan sanarwa ya biyo bayan alanta niyyar takara kujerar shugaban kasa a 2023 da Yemi Osinbajo yayi ranar Litnin.

Yayin hira da manema labarai ranar Talata, Laolu Akande, ya bayyana cewa Osinbajo ya mayar da mambancinsa na APC jihar Osun, rahoton SR.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mataimakin shugaban ƙasa zai yi buɗe bakin Azumi da Sanatocin Jam'iyyar APC

Akande yace Osinbajo ya karbi katinsa ne a gunduma ta 1, Ikenne, jihar Ogun ranar 9 ga Febrairu, 2021, riwayar Business Day.

Osinbajo ya fita da APC ta Legas, ya koma ta jihar Ogun: Mai magana da yawunsa
Osinbajo ya fita da APC ta Legas, ya koma ta jihar Ogun: Mai magana da yawunsa
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin shugaban ƙasa ya ayyana aniyar gaje Buhari a 2023

Daga ƙarshe dai mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana nufinsa na neman takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Mataimakin shugaban ya ayyana aniyarsa a hukumance ne a wani gajeren Bidiyo da ya saka a shafinsa na Twitter bayan shafe watanni ana raɗe-raɗi.

Osinbajo ya ce:

"Ni a yau, tare da matuƙar ƙanƙan da kai ina mai ayyana nufina na neman ofishin shugaban ƙasan tarayya Najeriya a hukumance ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressive Congress (APC)."

Osinbajo ba ɗa na bane, Tinubu ya maida martani ga Mataimakin shugaban ƙasa

Kara karanta wannan

Hotuna: Kaakin majalisar wakilai, dimbin yan majalisa sun dira birnin Madina aikin Umrah

Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ba ɗan sa bane ba.

Tinubu ya yi wannan furucin ne a Abuja yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan gana wa da gwamnonin APC 12, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Taron wanda ya gudana a gidan gwamnan Kebbi dake Asokoro, a birnin Abuja, ya zo ne awanni bayan mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ayyana shiga tseren gaje Buhari a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng