Da Dumi-Dumi: Osinbajo zai yi buɗe baki tare da Sanatocin Jam'iyyar APC yau
- Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, zai gana da Sanatocin jam'iyya mai mulki APC yau Talata da yamma
- Osinbajo, a wata wasika da ya tura wa majalisa, ya gayyaci Sanatocin zuwa wurin buɗe bakin Azumi
- Wannan na zuwa ne bayan Osinbajo ya gana da Gwamnonin APC inda ya faɗa musu nufinsa na neman kujerar Buhari a 2023
Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Talata, zai karɓi baƙuncin Sanatocin jam'iyya mai mulki APC domin buɗa baki na Azumin yau.
Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙar gayyata da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta a zauren majalisa, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.
Wasikar gayyar shan ruwan na ɗauke da sa hannun jagoran majalisar dattawa, Yahaya Abdullahi.
Bayanai sun nuna cewa ana tsammanin zasu fara taron ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin yau a Aguda House.
Me mataimakin shugaban ya tattauna da gwamnoni?
A ranar Lahadi da ta shuɗe da yamma, Farfesa Osinbajo, ya karɓi bakuncin gwamnonin APC zuwa wurin Buɗe Baki, inda ya shaida musu burinsa na neman takarar shugaban ƙasa a babban zaben 2023 dake tafe.
Haka nan kuma ana tsammani mataimakin shugaban ƙasan zai sanar da Sanatocin APC kudirinsa a hukumance na gaje shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yayin ganawar su.
Osinbajo, a wani bidiyo da ya saki a shafinsa na Twitter, ya ɗauki alƙawarin kammala dukkan ayyukan da shugaba Buhari ya fara idan yan Najeriya suka ba shi dama.
Ya ce shekara Bakwai yana matsayin mataimakin shugaba, tsawon wannan lokaci ya samu kwarewar da zai ɗora daga inda Buhari zai tsaya.
A wani labarin kuma Jerin Mutanen da suka yi farin ciki da ayyana takarar mataimakin shugaban ƙasa
Ayyana shigarsa takara ya kawo ƙarshen watanni da aka kwashe ana yaɗa jita-jitar yana sha'awar gaje kujerar Buhari a 2023, kuma ta ƙara yawan masu hangen muƙamin.
Haka nan kuma lamarin ya sa zai yi gaba da gaba da tsohon Ogansa a jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya nuna alamun manufarsa tun farkon wannan shekara.
Asali: Legit.ng