Hotunan Katafariyar Gada Mai Hawa Uku da Ganduje Ke Ginawa a Kano, Babu Irinta a Faɗin Najeriya

Hotunan Katafariyar Gada Mai Hawa Uku da Ganduje Ke Ginawa a Kano, Babu Irinta a Faɗin Najeriya

  • Gwamnatin Kano na cigaba da aikin gada mai hawa uku a Shataletalen NNPC dake Anguwar Hotoro
  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce suna sa ran kammala aikin zuwa watan Satumba, an raɗa wa Gadar 'Muhammadu Buhari Interchange'
  • A halin yanzun, mutane na shan wahala wajen wucewa ta wurin kasancewar hanyar tana haɗa cunkoso

Kano - Gwamnatin Kano na cigaba da aikin gina wata katafariyar gada mai hawa uku wacce babu irinta a faɗin Najeriya a Anguwar Hotoro dake cikin ƙwaryar birnin Kano.

A wata sanarwa da gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya fitar a shafinsa na Facebook tare da Hotuna, ya ce aiki na cigaba da tafiya gadan-gadan.

Ya ce gadar wacce aka raɗa wa suna, "Muhammadu Buhari Interchange," aikinta ya yi nisa kuma gwamnati na gida ta ne a shataletalen NNPC dake Hotoro.

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Ja Hankali

A cewarsa gwamna Ganduje, gwamnatinsa ta kirkiri aikin ne domin rage Cunkoson ababen hawa da mutane ke fama da shi a wannan hanya.

Wani sashin sanarwan ta ce:

"Ana cigaba da aikin gina Katafiyar gada mai hawa Uku, wacce babu irinta a faɗin Najeriya, mai suna 'Muhammadu Buhari Interchange' kuma mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ke ginawa a Shataletalen NNPC Hotoro."
"Muna fatan aikin gadar zai rage yawan cunkoson ababen hawa da mutane ke fama da shi a hanyar da bunƙasa harkokin kasuwanci kasancewar mafi yawan jihohi ta nan suke shigowa domin kasuwanci."

Hotunan gadar Hotoro

Hotunan Gda mai hawa uku a Kano
Hotunan Katafiyar Gada mai hawa uku da Ganduje ke ginawa a Kano Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje CFR/facebook
Asali: Facebook

Hotunan Gada mai hawa uku a Kano
Hotunan Katafiyar Gada mai hawa uku da Ganduje ke ginawa a Kano Hoto: Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje CFR/facebook
Asali: Facebook

Gada mai hawa Uku.
Hotunan Katafiyar Gada mai hawa uku da Ganduje ke ginawa a Kano Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje CFR/facebook
Asali: Facebook

Gada mai hawa da Ganduje ke ginawa.
Hotunan Katafiyar Gada mai hawa uku da Ganduje ke ginawa a Kano Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje CFR/facebook
Asali: Facebook

Hotunan gada mai hawa Uku.
Hotunan Katafiyar Gada mai hawa uku da Ganduje ke ginawa a Kano Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje CFR/facebook
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta tattauwa da wani Bakano mazaunin Hotoro, Sanusi Isiyaku, kuma ya shaida wa wakiin mu cewa:

"Eh, maganar gaskiya aiki na tafiya gadan-gadan kuma da sauri, ga dukkan alamu gwamnati na son gama aikin nan kusa, sai dai mutane sun shiga ƙunci a hanyar duba da yawan ababen hawa dake wucewa."

Kara karanta wannan

An kai makura: Gwamnoni da shugabannin majalisa za su gana don tattauna batun tsaro

"Idan ka je wucewa ta wurin sai ka shafe sama da Awa ɗaya da rabi, wasu hanyoyin Anguwanni da mutane ke bi, sai kaga wasu sun haƙa rami dan kawai kar motoci su rinƙa bin layin."

Wakilin mu ya tambaye shi, kan yadda mutane suka ɗauki wannan aiki, Isiyaku ya ce:

"A ko da yaushe zaka samu ɓangare biyu na mutane, haka aikin Gadar nan, wasu na yaba wa, wasu kuma na kushewa, wasu kuma suna sanya siyasa a lamarin."

A wani labarin kuma bayan Tambuwal, Bala Muhammed da Wike, wani gwamnan PDP ayyana aniyar shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel , ya amsa kiran yan Najeriya na neman takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamnan ya ce ya karbi Fam ɗin da wata kungiyar kare hakkin ɗan Adam ta siya masa na sha'awar takara a PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: