Da Ɗumi-Ɗumi: Muna Bincike Kan Dalilin Lalacewar Lantarki Na Ƙasa, In Ji Gwamnatin Tarayya
1 - tsawon mintuna
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce tana bincike kan lalacewar wutar lantarki na kasa, rahoton Daily Trust.
Wutar lantarkin na kasa ya lalace ne a ranar Juma'a, hakan ya jefa kasar cikin duhu.
Amma, cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Makamashi ta fitar, ta ce tana aiki domin ganin an gyara matsalar.
Ta ce Hukumar Kula Da Lantarki na Kasa, NERC, mai kula da lantarkin na kasa, tana kan aikin ganin cewa an dawo da lantarkin.
"Muna son mu sanar da al'ummar kasa cewa an samu lalacewar wutar lantarki na kasa wanda ya faru misalin ƙarfe 1830hrs a ranar 8 ga watan Afrilun 2022, wanda hakan ya janyo rashin wuta a sassa daban-daban na kasar.
"Yayin da ake cikakken bincike don gano musababin yawaitar lalacewar wutan lantarkin, tuni an fara aikin gyaran wutar lantarkin a wasu sassa sun fara samun lantarki."
"Muna son mu tabbatar wa yan Najeriya cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki ba kama hannun yaro don ganin an yi sauye-sauye da saka hannun jari, ciki har da SCADA, da ke da muhimmanci don inganta lantarkin na kasa.
"Wannan ya yi daidai da tsarin Shugaban Kasa na bada muhimmanci ga sassan tattalin arzikin Najeriya masu muhimmanci, in ji sanarwar.
Wannan shine karo na uku da wutar lantarkin ke lalacewa amma Gwamnatin Tarayyar ta bada tabbacin cewa tana daukan matakan magance matsalar.
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng