Borno: Mahaifin Matar Gwamna Umaru Zulum ya riga mu gida gaskiya

Borno: Mahaifin Matar Gwamna Umaru Zulum ya riga mu gida gaskiya

  • Surukun gwamna Babagana Umaru Zulum ya rigamu gidan gaskiya ranar Jumu'a yana da shekaru 70 a duniya
  • Alhaji Kauna Bulama Kyari, mahaifi ga matar gwamnan, Falmata Umaru Zulum, ya rasu bayan fama da dogon jinya
  • A cewar Sakatariyar watsa labarai ga matar gwamna.ƙ, wannan babban rashi ne ga al'ummar jihar Borno baki ɗaya

Borno - Matar gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno, Dakta Falmata Umaru Zulum, ta yi rashin mahaifinta, Alhaji Kauna Bulama Kyari.

Ya rasu ne ya na da shekara 70 a duniya bayan ya sha fama da jinya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Matar gwamnan Borno, Falmata Babagana Zulum.
Borno: Mahaifin Matar Gwamna Umaru Zulum ya riga mu gida gaskiya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sakatariyar watsa labarai ta matar gwamnan, Hajiya Aisha Ngubdo, ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar jiya Jumu'a a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Matar gwamnan APC ta shiga jerin 'yan takarar sanata a jiharsu

Misis Ngubdo ta bayyana mamacin da mutumin kirki, da kulawa wanda mutane za su yi rashinsa ba wai iyalansa kaɗai ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Sakatariyar watsa labarai ta mace lamba ɗaya a Borno, Al'ummar jihar Borno sun yi babban rashi da zasu jima ba su mance da shi ba.

Ta kuma yi Addu'a ga mamacin da cewa Allah ya karbi baƙuncinsa, ya sa ransa ya samu nutsuwar haɗuwa da mahaliccinsa.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Yahaya Bello na jihar Ƙogi ya ce gwamnatinsa ta maida akalla mutum 2,000 miliyoniya a jihar

Ya yi wannan furucin ne a wurin taron ƙara wa juna sani game da manufofin GYB a siyasar Najeriya karo na biyu wanda ke gudana a Abuja.

Bello ya kuma bayyana shirinsa na zaɓar mace ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban ƙasa idan APC ta lamunce masa ta bashi tutar takara a zaɓen 2023, kuma ta amince ya zaɓi wanda zasu tafi tare.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Na maida mutum 2,000 sun zama Attajirai a jihata, Gwamnan Arewa dake son gaje Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262