Gonar kudi: Yadda matashi ya sayar da hoton tsaleliyar budurwa N600k a duniyar crypto
- Wani hazikin mai daukar hoto a Najeriya, Adisa Olashile, ya mayar da hoton wata tsaleliyar budurwa NFT, inda ya sayar da shi kan 0.35 Eth (N675,748.546)
- Mutumin da ya gode wa dandalin Foundation, inda ya sayar da hoton, ya kuma bayyana cewa har yanzu yana da sauran hotuna biyar na NFT
- 'Yan Najeriya da dama sun yi dafifi a sashen sharhi domin taya shi murna, yayin da wasu suka nemi ya koya musu fasahar NFT
Wani hazikin matashin madaukin hotuna a Najeriya, Adisa Olashile, ya yi amfani da karfin fasahar blockchain ta hada-hadar kudaden intanet wajen cika aljihunsa da kudi.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da ya sayar da hotunan wani tsohon makadi a kafar NFT ta OpenSea kan kudi sama da miliyan daya. Sannan ya yi alkawarin bai wa tsohon 50% na abin da ya samu.
Yadda ya siyar da hoton
A cikin wani rubutu a ranar Laraba, 6 ga Afrilu, hazikin matashin ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa ya siyar da hoton wata budurwa a matsayin Non-Fungible Token (NFT) akan Foundation, wata kafar musayar NFT.
An siya hoton ne ta tsarin NFT, @a5htr, akan 0.35 na Ethereum (ETH). Adisa ya bayyana cewa har yanzu yana da kwafi guda biyar da ya rage na sayarwa na hotunan.
A lokacin rubuta wannan rahoto, farashin 0.35 ETH/USDT a kasuwar kudin intanet ta Binance ya kai $1148.49 (N675,748.546) yayin da farashin ETH 1 ke kan $3281.42 (N1,930,721.9).
Ya kamata ku lura cewa farashin kudaden intanet basu da tabbas, komai zai iya faruwa idan aka samu sauyi a kasuwa.
A lokacin rubuta wannan rahoto, rubutun da ya yi a Twitter ya tattara dubban-dubatar martani tare da dangwale sama da 400.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:
@ClitonClit2 ya ce:
"Dan uwa ina DM dinka Ina bukatan taimakon ka akan NFT."
@Blackbody ya ce:
"Waw! Wani nasaran kuma, ina taya murna."
@teexels ya ce:
"Ina taya ka murna Adisa! Na san irin wannan! Kuma za a sayar da kai nan ba da dadewa ba!!! A halin yanzu ina da gwanjon wani kadan da ya rage! LFG."
@AnnaRostphoto ya ce:
"Na taya ka murna! Hoto mai kyau sosai!"
@tatchero ya ce:
"Kwarai kuwa! Ina taya ka murna dan dangi.!"
@Abiodunsax ya ce:
"Ina taya ka matukar murna dan uwa! Fatan karin nasara."
Abin da ka raina: Yadda matashi ya dauki hoton makadi, ya sayar N1.2m a duniyar Crypto
A wani labarin, wani matashi madaukin hotuna a Najeriya, Adisa Olashile, ya nuna daya daga cikin damammaki masu yawa na duniyar kudaden intanet wato blockchain da cryptocurrency ta kunsa.
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 1 ga Afrilu, Adisa ya ce ya dauki hotunan wani tsohon makadi wanda ya saba gani a hanyarsa ta zuwa hidimar ci gaban al’umma ta CDS ta NYSC.
A ranar Asabar, 2 ga Afrilu, madaukin hotunan ya hau Twitter inda ya bayyana cewa ya sauya hotunan tsohon makadin zuwa Non-Fungible Token (NFT) a kasuwar OpenSea kuma ya sayar da su akan 0.3 Ethereum (Eth) kowanne.
Asali: Legit.ng