Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari

Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Buhari ya ce yana da tabbacin yan Najeriya zasu cigaba da zaben jam'iyyar APC
  • A cewar Buhari, yana da wannan tabbaci ne saboda irin namijin kokarin da gwamnatin APC ta yiwa yan Najeriya
  • Shugaba Buhari ya hau mulki ne ranar 29 ga Mayu 2019 kuma zai sauka ranar 29 ga Mayu, 2023

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatin All Progressives Congress (APC) ta yiwa yan Najeriya namijin kokarin da ya cancanci su sake zabenta.

Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi aiki mai kyau musamman a bangaren aikin noma, gina tituna, ilmin ICT, da jin dadin yan Najeriya.

Ya baiwa yan Najeriya tabbacin cewa zai cigaba da karfafa demokradiyya a siyasa da jagoranci.

Shugaba Buhari
Yan Najeriya zasu zabi APC a 2023 saboda gwamnati na ta yi namijin kokari, Shugaba Buhari Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin sabon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, da gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, bisa jawabin da Garba Shehu ya saki.

Yace:

"Ya kamata muyi farin ciki jam'iyyarmu ta dinke barakarta domin fuskantar kalubalen dake gabanmu na zaben jihohi da na tarayya."
"Idan na yi waiwaye kan tsare-tsaren gwamnati na kan tattalin arziki, musamman wajen cigaban aikin noma, manyan ayyukan gine-gine, ICT da jin dadin al'umman da muka yiwa mata, matasa da masu nakasa, ina samun karfin gwiwan cewa yan Najeriya zasu cigaba da zaben APC."
"Gwamnatinmu na kokarin gyara kasar nan. Tsare-tsare da shirye-shiryenmu na kawo cigaba wa kasar nan da al'ummanta ne."

Shugaba Buhari ya kara da jinjinawa kwamitin rikon kwaryan Mai Mala Buni bisa nasarar taron gangamin da suka gudanar kuma ya musu godiya matuka.

Ya yi kira ga sabon shugaban jam'iyyar yayi tsayin daka kuma ya jajirce kamar yadda aka san shi.

Kara karanta wannan

PDP da APC sun yi babban rashi: Tsohon Sanata, tsaffin yan majalisa, mambobi 10,000 sun koma NNPP

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a ranar Alhamis ya yi kira ga yan Najeriya su godewa Shugaba Muhammadu Buhari bisa ayyukan layin dogon jirgin kasan da take a fadin tarayya.

Amaechi ya bayyana hakan ne a Abeokuta, jihar Ogun yayin taron kaddamar da sabbin motocin hayan da gwamnatin jihar ta saya, rahoton Daily Trust.

Ya ce duk da sukar Buhari da ake yi kan karban basussukan kudi, bai yi kasa a gwiwa wajen gina layukan dogo ba tun da ya hau mulki a 2015

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng