Da Duminsa: Yan bindiga sun kai kazamin hari Hedkwatar karamar hukuma a Anambra
- Yan bindiga sun kai hari Sakariyar karamar hukumar Aguata dake jihar Anambra yankin da gwamnan jihar ya fito
- Rahoto ya bayyana cewa maharan sun cinna wa wurin wuta, wasu mutane sun ce shaguna da yawa sun kone kurmus
- Kakakin yan sandan jihar yace tuni aka tura jami'ai yankin, amma ba bu cikakken bayani a halin yanzu
Anambra - Yan bindiga sun kai wani mummunan hari Sakatariyar ƙaramar hukumar Aguata ta jihar Anambra, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, wanda ya karɓi ragamar jihar a watan Maris, daga yankin Aguata ya fito.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun cinna wa Hedkwatar karamar hukumar wuta yayin harin wanda ya faru ranar Alhamis, 7 ga watan Afrilu, 2022.
Daily Trust ta tattaro cewa yan bindigan sun isa akan mashina, suka yi amfani da babbar Motar ɗaukar kaya wajen tsohe hanya, bayan haka suka shiga Sakatariyar suka cinna wuta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya ce da yawan Shagunan dake cikin Sakatariyar sun kone ƙurmus.
Ya ce mintuna kaɗan bayan yan ta'addan sun bar wurin, Dakarun soji suka iso domin kame wasu matasa yan asalin yankin.
Mutumin yace:
"Gidana yana kusa da Sakatariyar, mun ga duk abin da ya faru, yanzu haka muna karkashin gado da ƴaƴana, duk muna cikin tsoro. Ba mu da tabbacin ko lamarin ya rutsa da wasu."
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, yace tuni aka ƙara girke jami'an tsaro a yankin da abun ya faru.
Ya ce sun samu rahoton lamarin da ya shafi wuta kuma an sanar da Jami'an kwana-kwana yanzu haka sun isa wurin don shawo kan lamarin.
Kakakin yan sandan ya ce:
Innalillahi: Yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun kashe wani fitaccen Attajiri a Katsina da Azumi
"Mun tuntuɓi hukumar kashe gubara domin su shawo kan wutar kuma a halin yanzun ba zan iya ce komai ba, babu cikakken bayani kan abun da ya auku."
"Ba zan iya magana kan adadin mutanen da lamarin ya shafa ba, hakan zai biyo bayan mun ceci wurin."
A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari kauyuka huɗu da tsakar rana a Zamfara, rayuka sun salwanta
Yan bindiga sun sake kai hari kauyukan karamar hukumar Anka a jihar Zamfara da tsakar rana, sun kashe akalla mutum 17.
Wani mazaunin yankin, Hussaini, ya ce sun fito daga Sallar Azahar kenan suka hangi zuwan yan ta'addan, nan take suka yi takansu.
Asali: Legit.ng