Da Ɗuminsa: Babban Kwamandan Boko Haram, Ibn Kathir, Ya Miƙa Kansa Ga Sojoji

Da Ɗuminsa: Babban Kwamandan Boko Haram, Ibn Kathir, Ya Miƙa Kansa Ga Sojoji

  • Daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram, Saleh Mustapha, da aka fi sani da 'Ibn Kathir' ya mika kansa ga sojoji
  • Bernard Onyeuko, Direktan Watsa Labarai na Sojoji ne ya bayyana hakan yayin yi wa manema labarai jawabi a ranar Alhamis a Abuja
  • Onyeuko ya ce mika wuyan da Mustapha ya yi babban nasara ne ga sojojin Operation Hadin Kai da ke Bama a Jihar Borno

FCT, Abuja - Hedkwatar Tsaro ta Najeriya ta ce babban kwamandan kungiyar Boko Haram, Saleh Mustapha ya mika kansa ga dakarun Operation Hadin Kai, da ke arewa maso gabas.

Kawo yanzu yan ta'adda guda 51,114 ne suka mika wuya kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babban Kwamandan Boko Haram, Mustapha Ibn Kathir, ya mika wuya: DHQ

Da Ɗuminsa: Babban Kwamandan Boko Haram, Ibn Kathir, Ya Miƙa Kansa Ga Sojoji
Babban Kwamandan Boko Haram, Ibn Kathir, Ya Miƙa Wuya. Hoto: Channels Television.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Direktan Watsa Labarai na Sojoji, Bernard Onyeuko, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan dakarun sojojin tsakanin 25 ga watan Maris zuwa 7 ga watan Afrilu a ranar Alhami a Abuja.

Mr Onyeuko ya ce mika wuyan da Mustapha wanda aka fi sani da Ibn Kathir, wanda na hannun daman Qaid na Garin Ba-Abba ne, babban nasara ne ga sojojin da ke Bama, rahoton Daily Nigerian.

Ya kara da cewa kawo yanzu yan ta'adda 51,114 ne suka mika wuya, cikinsu akwai maza 11,398 da mata 15,381 sai yara 24,335 zuwa ranar 5 ga watan Afrilu.

A cewarsa tuni an dauki sunayen wadanda suka mika wuyan an adana, sannan farare hula da aka ceto an mika su ga hukumomin da ya dace kafin hada su da iyalansu.

Kara karanta wannan

Sun Gane Shayi Ruwa Ne: 'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

Sojojin sun yi nasarar kwato makamai da dama a hannun yan ta'adda, Onyeuko

Ya ce a cikin makonni biyu da suka gabata, sojojin sun kama tankar yaki, manyan bindigun yaki biyar da GTS uku sannan da bindigan AA guda uku.

Saura sun hada da motar da bam baya iya tada ta wato MRAP, motocci masu bindigu guda uku, MOWAG guda daya da RPG guda biyu.

Mr Onyeuko ya ce dakarun sojojin sun kuma kashe yan ta'adda da dama yayin da suka kama masu leken asirin yan ta'adda 11, 'yan sakon yan ta'adda 3 tare da ceto farar hula guda 30 da wasu nasarorin.

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164