Ina son Allah ya mun hisabi kan duk abin da harshe na ya faɗa, Sheikh Khalid
- Fitaccen malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Nuru Khalid, ya ce ya shirya fuskantar Hisabi ranar lahira kan huɗubarsa
- Shehin Malamin wanda ya rasa kujerar limacinsa a Abuja kan huɗubar sukar gwamnati, ya ce bai yi dana sani ba
- Kwanaki kaɗan bayan tsige shi, Malam Khalid ya samu wani muƙamin limanci duk a birnin Abuja
Abuja - Tsohon limamin Apo Legislative Quaters, Dakta Muhammad Nuru Khalid, ya ce a shirye yake Allah ya masa hisabi kan kalaman da ya faɗa.
Biyo bayan wata huɗuba da ya yi wacce kwamitin masallacin ke ganin ta yi tsauri ga gwamnati, da farko sun dakatar Sheikh Khalid daga baya kuma suka tunɓuke shi daga limanci.
Sheikh Khalid ya samu wani limanci a wani masallaci na daban a Abuja, amma lamarin ya jawo cece kuce a tsakanin yan Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta inda Shehin ke da dubbannin mabiya.
Da yake jawabi yayin zantawa da Trust TV, Khalid ya ce ya sake zama ya kalli huɗubarsa ta ranar Jumu'a kuma har yanzun yana kan bakarsa na kalaman da ya yi amfani da su.
Shehin Malami ya ce ya shirya tsayawa gaban Allah a ranar Lahira ya amsa tambayoyi kan maganganun da ya faɗa.
Sheikh Ƙhalid ya ce:
"Duk kalaman da kuka ji a wannan huɗuba daga bakina suka fito kuma na shirya tsayawa a kan su. Kuma ina Addu'a, Allah SWT ya sanya mun su a mizanin ayyuka na."
"Kuma ina Addu'a Allah ya bijiro mun da su a ranar Lahira, domin na yi imanin cewa suna tsagin kyawawan ayyuka."
Ko me Malamin ke son ya cimma wa?
Malamin ya ƙara da cewa duk wani kokari da yake yana yi ne domin kare martabar yan Najeriya.
"Ina kokarin kiyaye rayuwar yan Najeriya ne. Ina ƙoƙarin farfaɗo da ƙarfin gwamnati ne, ina son tuna musu demokariɗiyya ba tana nufin zaɓe bane kaɗai, mafi mahimmanci kare rayuka da dukiyoyi."
"Yana ɗaya daga cikin nauyin da ya rataya a wuyan duk wata gwamnati, bana ganin an yi kuskure. Amma duk wanda yake gani da gyara, yana da damar ya gyara mun."
A wani labarin kuma Kungiyar ASUU tace ba ta damu jami'o'in Najeriya su cigaba da zama kulle ba har dai gwamnati ta yi abunda ya dace
Kungiyar malaman jami'o'i a Najeriya ta ce ba zata janye yajin aikin da take ba har sai gwamanati ta cika mata bukatunta.
Shugaban ASUU na shiyyar Kalaba da ya ƙunshi wasu jihohi, Aniekan Brown, ya ce ASUU ba ta damu jami'o'i su cigaba da zama a kulle ba.
Asali: Legit.ng