Jerin sabbin jami’o’i 12 da FG ta amince da su da kuma jihohin da suke
A ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu ne majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i 12 masu zaman kansu.
Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya tabbatar da hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan zaman majalisar na ranar Laraba, jaridar The Cable ta rahoto.
Mohammed ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da baiwa sabbin jami’o’i Lasisi wanda zai kasance a karkashin kulawar jami’o’in da ke kasa.
Sabbin jami’o’i na a jihohin Kano, Naje, Gombe, Sokoto, Delta, Abia, Anambra da babbar birnin tarayya, Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito.
Legit Hausa ta tattaro jerin sabbin jami’o’in kamar haka:
1. Pen Resource University Gombe, jihar Gombe
2. Al-Ansar University, Maiduguri, jihar Borno
3. Margaret Lawrence I -University, jihar Delta
4. Khalifa Ishaku Rabiu University Kano, jihar Kano
5. Sports University Idumuje Ugboko, jihar Delta
6. Bala Ahmed University Kano
7. Saisa University of Medical Sciences and Technology, jihar Sokoto
8. Nigerian-British University Hasa, jihar Abia
9. Peter University Acina-Onene, jihar Anambra
10. Newgate University, Minna, jihar Neja
11. European University of Nigeria in Duboyi, Abuja
12. North-West University Sokoto
Ba zamu buɗe jami'o'in Najeriya ba har sai an yi abun da ya kamata, inji ASUU
Ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ta ce ko kaɗan ba ta damu ba dan jami'o'in Najeriya sun cigaba da zama a kulle har sai gwamnati ta yi abinda ya dace domin gyara harkar ilimi da walwalar ma'aikata da ɗalibai.
The Nation ta rahoto cewa ASUU reshen shiyyar Kalaba wanda ya haɗa jihohin Akwa ibom, Cross Riba, Abia da Ebonyi, ita ce ta bayyana matasayarta a wata sanarwa.
Asali: Legit.ng