Dan Sadau: Kwamiti ya fusata, ya kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin Abuja gaba daya

Dan Sadau: Kwamiti ya fusata, ya kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin Abuja gaba daya

  • Kwamtin masallaci ta ce gaba daya ta kori limamin Masallacin Apo dake Abuja, Sheikh Nuru Khalid
  • Shugaban kwamitin masallacin rukunin gidajen yan majalisu, Sanata Sa'idu Muhammad Dan Sadau ne ya sanar da sabon matakin da suka dauka
  • Ya ce sun kore shi ne gaba daya saboda ya ki yin nadama bayan an dakatar da shi

Abuja - Kwamitin jagorancin masallacin rukunin gidajen yan majalisu da ke unguwar Apo a birnin tarayya Abuja, sun ce gaba daya sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Masallacin.

Shugaban kwamitin, Sanata Sa'idu Muhammad Dan Sadau ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilu.

Dan Sadau: Kwamiti ya fusata ya kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin Apo gaba daya
Dan Sadau: Kwamiti ya fusata ya kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin Apo gaba daya Hoto: newsdigest.ng
Asali: UGC

Dan Sadau ya shaida wa shahin Hausa na BBC cewa sun dauki sabon matakin ne bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid din ne a ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Nasan za a rina: Limamin masallacin UniAbuja ya yi martani kan dakatar Sheikh Nuru Khalid

Dalilin daukar sabon mataki na korarsa gaba daya

Matakin korar nasa na kunshe ne a cikin wata takarda da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin dauke da sa hannun Sanata Dan Sadau da aka aike wa Digital Imam.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Dan sadau ya kuma jadadda cewar an dauki matakin korarsa ne gaba daya sakamakon rashin nadamar da Shehin Malamin ya nuna bayan dakatar da shi da aka yi.

Nasan za a rina: Limamin masallacin UniAbuja ya yi martani kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid

A gefe guda, babban limamin masallacin jami'ar Abuja, Farfesa Taofiq Azeez, ya bukaci dakataccen limamin masallacin Apo, Shiekh Nuru Khalid, da kada ya bari gwiwarsa tayi sanyi kan halin da yake ciki a yanzu.

Legit Hausa ta rahoto yadda aka dakatar da Sheikh Khalid bayan wani wa'azi da ya yi a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Babu hankali a lamarin: Martanin Shehu Sani da wasu 'yan Najeriya kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid

Da yake magana a ranar Lahadi a taron Ramadana da kungiyar Al-Habibiyyah ta shirya, Farfesa Azeez ya ce dakatarwar da aka yiwa Sheikh Khalid ba abun mamaki bane, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng