Ba zan ci kudinku ko kwandala ba: Gwamnan PDP ya yiwa 'yan jiharsa alkawari
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa ba zai taba iya daukar kudi daga hakkin mutanen jihar sa ba
- Makinde ya ba da tabbacin cewa ba za a taba daukar kudin mutanen Oyo a sanya cikin asusunsa na zaman kansa ba ko ta halin kaka
- Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan zargin da ake yi wa gwamnatinsa kan kwangilar naira miliyan 998 ga daliban makarantun sakandare
Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce ba zai taba cire wa kansa kudi daga kudin mutanen Oyo ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan zargin da ake yi wa gwamnatin jihar Oyo na kara kudin kwangilar naira miliyan 998 ta littafan rubutun daliban makarantun sakandare.
Ya tafi shafinsa na Twitter domin karin haske, kuma ya ba da tabbacin tsarkake aikinsa ta hanyar wani sako da ya wallafa a ranar Litinin, 4 ga Afrilu.
Martaninsa a shafin Twitter
A ranar Lahadi, 3 ga watan Afrilu, Makinde, ya yi ikrarin yin murabus idan zargin ya zama gaskiya.
Dan siyasar ya zargi wasu miyagun mutane da ke son ganin sun bata sunan gwamnatinsa. Ya yi jawabi ne a wajen bikin cikar wani gidan rediyo mai zaman kansa mai suna Agidigbo 88.7FM da aka gudanar a cibiyar taron kasa da kasa, ICC., Ibadan.
Ya ce zarge-zargen kan kudin kwangilar, magudi da kuma dambarwa game da kwangilar da ake yi wa gwamnatinsa ba gaskiya ba ne, inda ya dage cewa idan aka gudanar da cikakken bincike aka gano gaskiya ne, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sauka daga kujerarsa.
'Yan siyasan PDP ne suka sankame albashin sojoji a aljifansu, inji gwamnatin Buhari
A wani labarib, fadar shugaban kasa ta sake magana kan wasu daga gazawar da tsohuwar gwamnatin PDP ta yi a karkashin shugabanninta na tsawon shekaru.
A wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar, fadar ta yi zargin cewa a tsawon shekaru 16 da PDP ta yi tana mulkin kasar, sojojin Najeriya na cike da tsananin kunci.
Sanarwar da jaridar Punch ta gani ta kara da cewa a lokacin albashin sojoji ya shiga aljihun 'yan siyasar PDP yayin da sojoji suke ta mutuwa a fagen fama saboda ba su da kayan aikin tunkarar 'yan ta'adda.
Asali: Legit.ng