Da dumi-dumi: Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista - Buhari ga kamfanonin sadarwa

Da dumi-dumi: Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista - Buhari ga kamfanonin sadarwa

  • Yan Najeriya da basu riga sun yi rijistan layukansu tare da kamfanin sadarwa ta NCC ba za su hadu da gagarumin cikas daga Litinin, 4 ga watan Afrilu
  • Gwamnatin tarayya ta bukaci daukacin kamfanonin wayar sadarwa da su hana layukan da babu rijista a kasar yin kiran waya
  • Sakamakon haka, daga yau Litinin, kiran waya ba za su fita ba daga dukkanin layukan da abun ya shafa

Gwamnatin tarayya ta umurci kamfanonin sadarwa da su hana duk wani kiraye-kirayen waya fita daga lauyukan da ba a hada da NIN ba daga yau Litinin, 4 ga watan Afrilun 2022, rahoton Vanguard.

Layukan da abun ya shafa sune wadanda ba a riga an yiwa rijita tare da hada su da lambar shaidar dan kasa ba wato NIN.

Da dumi-dumi: Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista- Buhari ga kamfanonin sadarwa
Da dumi-dumi: Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista- Buhari ga kamfanonin sadarwa
Asali: Original

Ikechukwu Adinde, daraktan hulda da jama’a na NCC da Kayode Adegoke, shugaban sashen sadarwa na hukumar NIMC ne suka bayyana hakan a wata sanarwa ta hadin gwiwa a ranar Litinin, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun bindige dan kwamishinan tsaron Zamfara lokacin buda baki

“A tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, ya bayar da umurnin domin aiwatar da shi da kuma fara shirin a watan Disamban 2020, daga cikin manufofin gwamnatin na tsaro da zamantakewa. An sha tsawaita wa’adin da aka bayar na hada lambar NIN da layukan sim sau da dama domin baiwa yan Najeriya damar bin wannan doka cikin yanci. FG ta kuma yi la’akari da kiraye-kirayen da kungiyoyi da dama – kungiyar kamfanonin sadarwa masu lasisi ta Najeriya (ALTON), kungiyoyin jama’a, kungiyoyin kwararru da sauransu suka yi domin kara wa’adin a baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Saboda haka, shugaban kasa ya amince da bukatun masu yawa don tsawaita wa’adin hada NIN da layukan sim. Sai dai a wannan gaba da ake ciki, gwamnati ta kaddara cewa aiwatar da manufar hada NIN da sim na iya ci gaba, saboda an riga an kammala komai domin tabbatar da ganin yan kasa da mazauna sun ba shirin hadin kai. Aiwatarwar yana da tasiri kan dabarun gwamnati musamman a bangarorin tsaro da zamantakewa da kuma tattalin arziki.”

Kara karanta wannan

Dakatar da Sheikh Nuru Khalid: Kungiyoyi sun yi martani masu zafi

Gwamnatin Buhari ta kashe Naira Biliyan 157 a aikin gina babbar gadar Neja-Delta

A wani labari na daban, Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta ce kawo yanzu an batar da kudi har N157bn a aikin gadar nan ta Second Niger.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ministar ta na wannan jawabi yayin da ta ziyarci wajen wannan aiki tare da shugabannin hukumar NSIA ta kasa a ranar Asabar.

Zainab Ahmed ta kai ziyara domin ganin yadda aikin yake tafiya ne tare da Farouk Gumel da Uche Orji wanda shi ne babban darektan NSIA da ke wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng